Takaitaccen tarihin kofofin Kano

Takaitaccen tarihin kofofin Kano

Kofofin Kano guda goma sha uku, sun samo asali fiye da shekaru dubu da suka wuce, tun zamanin Bagauda wanda ya fara gina kofofin Kano, wato zamanin Sarki Warisi, wanda shine ya fara gina Badala.

Tarihi ya nuna cewa a shekara ta dubu daya da dari uku (1300AH), ana da kofofi guda shida a, sai a karni na goma sha biyar, zamanin Sarki Muhammadu Rumfa aka kara kofofi guda hudu, sannan zamanin Sarki na Zaki aka kara kofofi guda uku.

Tarihi ya nuna cewa bayan zuwan Turawa sai aka kara kofofi guda biyu, wato Kofar Famfo da Sabuwar Kofa.

Wani masanin tarihin masarauta dake jami’ar Bayero ta Kano, Dr. Tijjani Muhammad Naniya ya bayyanawa taskar VOA dalilin kafa kofofin Kano.

“An kafa sune a yanayi na kasa wacce take shimfidaddiya, sadarwa tana da sauki, kuma an kafa su a yanki mai arzikin ruwa, mai arzikin noma, mai arzikin ma’adanai, to dole mutane za su so su zo wajen domin su ci albarkar wajen. Hakan sai ya kawo za’a iya kawo farmaki na yaki.

“Waje da yake a shimfide baka da tsaro to dole sai ka nemawa kanka tsaro, tsaron da zaka yi shine ka yiwa kanka katanga, ka kare kanka, to wannan shine asalin yin Badala.

“To kuma idan kayi Badala ka rufe ko’ina babu hanyar wucewa hakan sai ya zama matsala, to shine yasa aka yi kofofi.”

Ya kara da cewa kowacce kofa na da Maigadinta wanda ake kira da suna 'Sarkin Kofa'.

“Kamar Kwamanda ne na sojoji, kuma akwai sojoji a karkashinsa, shiyasa duk wata kofa zaka ga akwai gidaje na Sarkin Kofa da kuma Dakarunsa, koda wata matsala za ta taso, ko idan za’a kawowa Kano farmaki, to kafin a kawo sojoji daga cikin gari, to su sojojin da yake tare da su za su yi maganin abin,” in ji Dr. Tijjani.

Ga jerin kofofin Kano:

Kofar Gadon kaya

Kofar duka wuya

Kofar Kabuga

Kofar Dawanau

Kofar Dan agundi

Kofar Mata

Kofar Ruwa

Kofar Waika

Kofar Na'isa

Kofar Nasarawa

Kofar Famfo

Kofar Mazugal

Sabuwar kofa

Kofar Wambai

Kofar Kansakali

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng