Fizgen waya: Yadda jama'a suka taimakawa 'yan sanda wajen cafke barawo

Fizgen waya: Yadda jama'a suka taimakawa 'yan sanda wajen cafke barawo

Wani magidanci mai da daya, wanda ‘yan sanda suka kwatanta da dan fashin da ba zai taba tuba ba, ya shiga hannun runduna ta musamman ta ‘yan sandan jihar Legas, a kan zarginsa da ake da kwacen wayoyi daga hannun mutane.

Wanda ake zargin mai suna Tunde Ajeigbe, kamar yadda ‘yan sandan suka sanar, an fara kama shi ne da wannan laifin a 2017 kuma har yayi zaman gidan kaso.

An gano cewa, wanda ake zargin mai shekaru 27 tare da wasu mutane biyu sun hada kai wajen satar babur a yankin 7Up dake Legas. Ajeigbe ya daka tsalle daga babur din satar inda ya kwace waya daga hannun wani fasinja a cikin motar haya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Bala Elkana ya tabbatar da cafke wanda ake zargin. Ya bayyana yadda wanda ake zargin ya koma kan babur din tare da ‘yan uwansa bayan ya fizge wayar.

Elkana ya bayyana cewa, basu samu sa’a ba ranar saboda rundunar ‘yan sandan na kusa kuma sun bi su har gadar Otedola, inda sauran jami’ansu dake kasan gadar suka taimaka musu wajen bin wadanda ake zargin.

DUBA WANNAN: Saratu Gidado ta zama jakadiyar tallafawa mabukata

Ya ce, hakan yasa wadanda ake zargin suka yasar da babur din tare da fadawa daji amma sai ‘yan sandan suka yi nasarar cafke Ajeigbe.

“An taba kamani a Ojota bayan da na kwace wayar wata budurwa kuma aka gurfanar dani gaban kuliya. An tura ni gidan kaso amma na fito a ranar 19 ga watan Nuwamba, 2019. Na kasa komawa matata da da na,” in ji shi.

Ya ce ya koma gidan da yake amma bai tarar da matarshi da dan shi ba. Hakazalika babu komai nashi. A don haka ne ya koma ruwa.

“Na koma kasan gada wajen abokaina inda suka bani abinci da kaya kuma daga bisani muka koma harkarmu ta da.” Ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel