Kotu Ta Daure Ministan Buhari Shekaru 75 a Gidan Kaso kan Badakalar N33.8bn
- Wata kotu a Abuja ta yanke hukunci game da tuhumar tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman kan badakalar kudi
- Kotun ta yanke masa hukuncin ne bayan samunsa da laifin satar kusan N33.8bn na kudaden gwamnati
- Alkalin kotu ya tabbatar da laifukan damfara da safarar kudi 12 da EFCC ta gabatar, tare da yanke hukunci ba tare da zabin tara ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kotu a Abuja ta yanke wa tsohon ministan makamashi, Saleh Mamman hukunci kan zargin badakalar N33.8bn.
Kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 75 bisa zargin satar kudaden gwamnati da suka kai kusan N33.8bn.

Source: Twitter
Hukuncin da kotu ta yanke kan Saleh Mamman
Alkalin kotu ya ce an tabbatar da laifuffukan damfara da safarar kudi 12 da EFCC ta gabatar, inda aka ba shi hukunci mai gudana ba tare da zabin tara ba, cewar Vanguard.
An kuma umarci kwace kadarori da kudaden kasashen waje da aka gano a hannunsa, tare da ba da umarnin kamo shi ta hanyar Interpol saboda ya gudu
Tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, ya fuskanci hukuncin daurin shekaru 75 daga babbar kotun tarayya da ke Abuja kan zargin rashawa da almundahana.
Alkalin kotu, Mai Shari’a James Omotosho, ya yanke hukunci kan dukkanin tuhume-tuhume 12 da hukumar EFCC ta gabatar kan laifukan damfara da safarar kudi.
Kotun ta ce an tabbatar da laifuffkan ba tare da wata shakka ba, inda aka yanke masa shekaru bakwai kan kowanne daga cikin manyan tuhume-tuhume 10.
Haka kuma an yanke masa shekaru uku da biyu kan wasu tuhume-tuhume biyu, tare da umarnin cewa hukuncin zai gudana gaba daya ba tare da sassauci ba.
An ba shi damar biyan tara na Naira miliyan 10 kawai kan daya daga cikin tuhume-tuhume, yayin da sauran suka kasance daurin kurkuku kai tsaye.
Kotun ta kuma kwace kudaden kasashen waje da aka gano a hannunsa, tare da kadarori hudu masu daraja a birnin Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa an same shi da laifin biyan dalar Amurka 655,700 wajen sayen fili a Abuja ba tare da banki ba.
An kuma same shi da karkatar da kudaden ayyukan wutar lantarki na Mambilla da Zungeru zuwa wasu hannaye ba bisa ka’ida ba.

Source: UGC
Matsalar da badakalar ta jawo wa Najeriya
Alkalin kotu ya ce hujjojin gwamnati sun yi karfi sosai yayin da bangaren kariya ya gaza gabatar da hujja mai gamsarwa.
Ya ce a matsayin minista, Saleh Mamman ya kasa barin tarihi mai kyau, maimakon haka ya yi amfani da mukaminsa wajen cin gajiyar jama’a.
A cewarsa, wannan na daga cikin dalilan da suka sa wutar lantarki ta ci gaba da zama matsala a Najeriya har yanzu.
Kotun ta kuma ce za a fara kirga hukuncin ne daga ranar da aka kama shi, yayin da aka bayar da umarnin kamo shi ta hanyar Interpol.
Lauyan sa ya ce bai san inda yake ba, kuma kiran wayarsa ba ta shiga, yayin da ake ci gaba da neman shi a hukumance.
'Ya kamata a daure ministocin Buhari' - Jigon APC
Mun ba ku labarin cewa jigon APC, Alwan Hassan ya yi kaca-kaca da kusan duka ministocin da suka yi aiki karkashin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Alwan ya bayyana cewa kamata ya yi zuwa yanzu sama da kaso 90 na ministocin marigayi Buhari na daure a gidan gyaran hali.
Ya ce ba a taba samun wani lokaci da ake sakar wa kowane minista kasafin kudi ba tare da sanya masa iso ba kamar lokacin Buhari.
Asali: Legit.ng


