Martanin PDP ga Buhari: Kai ne jagoran masu zuwa kasar waje domin duba lafiyarsu

Martanin PDP ga Buhari: Kai ne jagoran masu zuwa kasar waje domin duba lafiyarsu

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi kira ka shugaban kasa Muhammadu Buhari daya daina fita kasashen waje domin duba lafiyarsa kamar yadda ya yi kira ga yan Najeriya, domin ya kasance shugaba nagari abin koyi.

Jaridar The Cable ta ruwaito PDP ta bayyana haka ne cikin wani martani da ta aika ma shugaban kasa Muhammadu Buhari game da kiran da ya yi ma yan Najriya dasu daina fita kasashen waje ana duba lafiyarsu.

KU KARANTA: Ashsha! Yan fashin teku sun yi garkuwa da mutane 3, sun kashe Sojojin Najeriya 3

Buhari ya bayyana haka ne a yayin bikin mika wasu manyan gine gine da aka kammala aikinsu ga asibitin koyarwa na jami’ar Alex Ekwueme dake garin Abakaliki a ranar Juma’a, 3 ga watan Janairu, inda ya samu wakilcin ministan kimiyya da fasaha, Ogbannaya Onu.

Idan mai karatu zai iya tunawa, shugaban kasa Buhari ya yi tafiye tafiye da dama zuwa kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa tun bayan darewa mukamin shugaban kasar Najeriya.

Sai dai cikin wata sanarwa da PDP ta fitar ta bakin mai magana da yawunta, Kola Ologbondiyan, ta bayyana Buhari a matsayin jagora, kuma shugaban masu fita kasar waje duba lafiya.

“Wannan ya nuna matsayin da gwamnati ta kai wajen yaudarar yan Najeriya, jam’iyyarmu ta bayyana haka a matsayin abin dariya kuma abin takaici yadda shugaban da yake fita kasar waje don duba lafiyarsa, kuma ya gagara inganta asibitocin Najeriya zai yi kira ga yan kasa dasu daina fita duba lafiyarsu a kasashen waje.

“Duk da cewa PDP ba ta amince da yawan fita kasar waje duba lafiya musamman ga shuwagabanni ba, amma jam’iyyarmu na da ra’ayin duk shugaban daya gaza wajen inganta kiwon lafiya ba shi da hurumin hana mutane fita kasar waje duba lafiyarsu.

“Abin haushin ma duk wasu tsare tsaren tabbatar da ingantaccen kiwon lafiya da gwamnatin PDP ta tanadar sun lalace a karkashin sa idon gwamnatin APC sakamakon nuna halin ko in kula dasu.” Inji shi.

Daga karshe PDP ta yi kira ga Buhari da ya dauki kwararan mataka don ganin ya inganta tsarin kiwon lafiya ta yadda yan Najeriya zasu samu daman duba lafiyarsu a gida Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel