An Gwabza Faɗa tsakanin Jami'an Kwastam da Ƴan Ta'addan Lakurawa, An Rasa Rayuka

An Gwabza Faɗa tsakanin Jami'an Kwastam da Ƴan Ta'addan Lakurawa, An Rasa Rayuka

  • Jami’an Kwastam biyu sun rasa rayukansu yayin artabu da ake zargin sun yi da ‘yan ta’addar Lakurawa a Kebbi
  • Shugaban Kwastam, Bashir Adeniyi, ya ce jami’an sun mutu ne yayin da suke dakile hare-haren ‘yan ta'addan
  • Hukumar Kwastam ta jaddada cewa mutuwar jami’an ba za ta hana ci gaba da yaki da masu aikata laifuffuka ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kebbi - Wasu jami’an hukumar Kwastam ta Najeriya guda biyu sun rasa rayukansu yayin wata arangama da ƴan ta'addar da ake zargin Lakurawa ne a Kebbi.

Shugaban hukumar Kwastam, Bashir Adeniyi, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da aka gudanar a jami’ar Ilorin ranar Laraba.

'Yan ta'addar Lakurawa sun kashe jami'an Kwastam a Kebbi.
Jami'an hukumar Kwastam sun yi sahu sahu don girmama shugaban su. Hoto: @CustomsNG
Source: Twitter

Arangamar Lakurawa da jami'an Kwastam

Rahotanni sun nuna cewa jami’an da suka mutu sun hada da ASC Bamigboye da DSC Dom, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan tadiye yaransa a tantancewar APC, Fubara ya magantu kan alakarsa da jam'iyya

An ce jami’an sun mutu ne da misalin karfe 3:00 na safiyar Laraba yayin wani farmaki da suka kai domin dakile ayyukan Lakurawa da ake zargi da ta’addanci a yankin Kebbi.

Bashir Adeniyi ya bayyana cewa jami’an sun sadaukar da rayuwarsu ne yayin kare al’umma daga barazanar ‘yan ta’adda, in ji rahoton Punch.

Jimamin mutuwar jami'an Kwastam

Da yake jawabi a wajen taron kasa da kasa da sashen koyar da kimiyyar sadarwa da tattara bayanai na jami'ar jami’ar Ilorin ta shirya tare da hadin gwiwar sashen Philogy na jami'ar RUDN da ke kasar Rasha, shugaban Kwastam ya bayyana bakin cikinsa kan mutuwar jami’an.

“A safiyar yau jami’an Hukumar Kwastam biyu sun sadaukar da rayuwarsu yayin dakile barazanar ‘yan ta’addar Lakurawa a Kebbi.”

Ya kara da cewa jami’an kwastam na taka muhimmiyar rawa wajen ayyukan tsaro tare da jami’an soji a yankunan iyaka.

Jami'an hukumar Kwastam sun mutu a yaki da yan ta'addar Lakurawa a Kabbi
Taswirar Kebbi, jihar da ƴan ta'addar Lakurawa suka kashe jami'an Kwastam. Hoto: Legit.ng
Source: Original

“Kwastam na kare iyakokin kasa” - Adeniyi

Adeniyi ya ce bayan jami’an soji, hukumar kwastam ce ke ci gaba da zama garkuwa ga wasu yankunan kan iyaka da ke fama da hare-haren masu aikata laifuffuka.

Ya bayyana cewa ya riga ya isa Ilorin kafin samun rahoton harin, yana mai cewa da labarin ya zo masa tun farko, watakila da ya soke halartar taron.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta faɗi tarkon da ta ke yi wa tubabbun Boko Haram da Kur'ani

Sai dai ya tabbatar da cewa mutuwar jami’an ba za ta rage wa hukumar kwarin gwiwa wajen ci gaba da yaki da masu aikata laifuka a kan iyakokin Najeriya ba.

Bayan jawabin shugaban kwastam, mahalarta taron sun tsaya domin yin shiru na minti guda wajen girmama jami’an da suka rasu.

Lakurawa sun yi ta'addanci a Kebbi

A wani labarin, mun ruwaito cewa an shiga jimami a jihar Kebbi bayan da 'yan ta'addan kungiyar Lakurawa suka kai wani harin ta'addanci a wasu kauyuka.

Tsagerun 'yan ta'addan sun hallaka mutane sama da 30 bayan sun kai hare-hare a kauyukan da ke yankin Arewacin jihar.

Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta hannun mai magana da yawun bakinta, ta yi karin bayani kan munanan hare-haren na 'yan ta'addan Lakurawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com