Kisan kwamandan Iran: Mayakan Hezbollah sun kai farmaki a ofishin jakadancin Amurka

Kisan kwamandan Iran: Mayakan Hezbollah sun kai farmaki a ofishin jakadancin Amurka

A cigaba da takalar juna tsakanin kasar Amurka da kasar Iran, wata kungiyar Shia ta jefa wasu rokokin bamabamai guda biyu zuwa ga ofishin jakadancin kasar Amurka dake Baghdad a kasar Iraqi.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito wannan kungiya mai suna Kataeb Hezbollah ta dauki alhakin jefa rokokin bayan cikar wa’adin da ta baiwa dakarun Sojin kasar Iraqi dasu tashi daga duk wani sansani da suke zama tare da Sojojin Amurka zuwa karfe 5 na yammacin Lahadi.

KU KARANTA: Ashsha! Yan fashin teku sun yi garkuwa da mutane 3, sun kashe Sojojin Najeriya 3

Sai dai shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa rokokin basu kai ga fadawa ofishin jakadancin ba, illa dai sun fadi a gab da ofishin ne. wannan shi ne karo na 14 da ake harba rokoki ga sansanonin kasar Amurka dake Iraqi a cikin watanni biyu.

A wani labarin kuma, Legit.ng ta ruwaito a wani mataki na kan da garki, ko kuma kamar yadda masu iya magana kan ce, wai “rigakafi ya fi magani” Babban sufetan Yansandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu ya umarci jami’an Yansandan Najeriya su zauna a cikin shiri ta yadda komai ta fanjama fanjam!

IG Adamu ya bayar da wannan umarni ne biyo bayan kisan wani babban kwamandan yaki na kasar Iran da gwamnatin kasar Amurka ta kashe shi a makon da ta gabata, inda yace sun samu labarin akwai wasu dake shirin tayar da hankulan jama’a a Najeriya tare da yi ma gwamnatin Najeriya zagon kasa.

Da wannan ne IG Adamu ya umarci kwamishinonin Yansanda, da AIG na shiyya shiyya da su tabbata sun sanya idanu sosai domin tabbatar da tsaron dukiya da rayukan al’umma a duk fadin kasar nan.

Sanarwar wanda mai magana da yawun rundunar Yansandan Najeriya, DCP Frank Mba ya fitar ta bayyana an umarci kwamandojin Yansanda su tabbata sun tura jami’ansu na fili da na boye zuwa wuraren da suka kamata don samar da isashshen tsaro.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel