Mu yi addu'a Mutumin kirki ya karbi Shugaban kasa Buhari a 2023 – Tunde Bakare

Mu yi addu'a Mutumin kirki ya karbi Shugaban kasa Buhari a 2023 – Tunde Bakare

Shugaban cocin Latter Rain Assembly, Fasto Tunde Bakare, ya ba shugaban Najeriya Muhammadu Buhari shawarar ya tsaida Magajinsa.

Faston da ya tsayawa Muhammadu Buhari a matsayin ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar CPC a 2011, ya yi magana game da 2023.

Tunde Bakare ya roki ‘Yan Najeriya su yi addu’a ta yadda mulki ba zai koma hannun Barayi da Miyagu idan har Buhari ya kammala wa’adinsa ba.

A jawabinsa ga ‘Yan kasa, Malamin addinin Kiristar, ya yi kira ga shugaba Buhari ya kafa tubali masu karfi da za su sa nagari ya gaje sa a nan gaba.

Bakare ya yi wa wannan jawabi na sa take da ‘Bankado ainihin Makiyan Najeriya’. Faston ya yi wannan bayani ne a jiya Lahadi, 5 ga Watan Junairu.

KU KARANTA: Ni zan karbi mulkin Najeriya a 2023 bayan Buhari - Bakare

Mu yi addu'a Mutumin kirki ya karbi Shugaban kasa Buhari a 2023 – Tunde Bakare
Bakare ya nemi Buhari ya tsaida mutumin da zai yi bakin kokarinsa
Asali: Depositphotos

A cewar ‘Dan siyasar, wani babban nauyin da ke kan shugaban kasar shi ne kafa turbar da za ta sa a samu jerin shugabannin da za su kai kasar ga ci.

Fasto Bakare ya ce: “Ubangiji ya yarda da Magaji. Duk wanda ya ke mulki, amma ba ya damuwa da wanda zai gaje shi, ya na rusa tarihin da ya kafa.”

“Dalili kuwa shi ne, wanda zai zo bayan ka, zai iya ruguza duk abubuwan da ka yi. Sai mu roki Ubangiji ya samu mu dace da Magaji.” Inji Malamin.

Ya roki Ubangiji ya sa Buhari ya mika ragamar mulki ga masu kishin kasa, ba Barayi, Kuraye, Marasa gaskiya da kuma wadanda su ke da giyar mulki ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel