Ku gayawa gwamna Fintiri ya ceceni - Shugaban CAN da Boko Haram ta sace yayi magana (Bidiyo)

Ku gayawa gwamna Fintiri ya ceceni - Shugaban CAN da Boko Haram ta sace yayi magana (Bidiyo)

Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya CAN, a karamar hukumar Michika ta jihar Adamawa, Rabaran Lawan Andimi, da yan Boko Haram suka sace ya yi kira gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri, ya cecesa.

A wani bidiyon da shahrarren dan jarida, Ahmad Salkida, ya saki, Rabaran Andimi ya ce yan ta'addan basu ci zarafinsa tun lokacin da suka saceshi.

Yace: "Ban taba yanke zuciya ba, saboda duk halin da dan Adam ya samu kansa, yana hannun Allah."

"Ina kira ka abokan aikina, rabarori, musamman shugabanmu, Rabaran Joel Billy, wanda babban mutum ne, ya taimaka ya yiwa gwamna Umaru Jibrilla (Fintiri) magana domin a sakeni."

A Ranar Alhamis, 2 ga Watan Junairu, 2019, ‘Yan Boko Haram sun kai hari, har su ka sace babban Faston da ke Kauyen na Michika.

Hakimin Michika, Ngida Kwace, shi ne ya bayyanawa Mai girma Mataimakin gwamna, Crowther Seth, wannan a lokacin da ya kawo masu ziyara.

Mista Crowther Seth ya ziyarci Garin Michika ne a jiya Ranar Asabar, bayan samun labarin ta’adin da ‘Yan Boko Haram su ka yi a wannan Yankin.

Kalli bidiyon:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel