Masu garkuwa sun yi awon gaba da matafiya guda 10, sun kashe 1 a Taraba

Masu garkuwa sun yi awon gaba da matafiya guda 10, sun kashe 1 a Taraba

Akalla mutum ne guda daya ne ya rasa ransa yayin da wasu gungun miyagu yan bindigan daji suka kai farmaki ga wata ayarin matafiya a jahar Taraba, inda suka tasa keyar mutane 10 da nufin garkuwa da su.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito shugaban riko na karamar hukumar Wukari, Daniel Grace ya tabbatar mata da haka cikin wani hirar wayar tarho da ta yi da shi a ranar Lahadi, inda yace lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 na daren Asabar.

KU KARANTA: Martanin PDP ga Buhari: Kai ne jagoran masu zuwa kasar waje domin duba lafiyarsu

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ciyaman Daniel yace yan bindigan sun tare da matafiyan ne a tsakanin kauyukan Bantaje da Mahanga cikin garin Chedia na karamar hukumar Wukari, ya kara da cewa sun dauke fasinjoji 10 da wayar direban.

Shi ma wani direba mai suna Yunana Baba ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace yan bindigan sun tafi da fasinjojinsa guda hudu, kuma yace ya ga motoci guda biyu a fake a gefen hanya, a kokarinsa na binciken abin dake faruwa ne sai kawai ya ga an nuna masa bakin bindiga, aka umarce shi ya tsaya.

“Na san cewa Sojoji ne suke zama a wannan wuri, a lokacin da nake karasawa wurin sai na ga wasu motoci irin nawa guda biyu a fake a gefen hanya, kwatsam sai wani mutumi sanye da kakin Sojoji fuskarsa a rufe ya nemi na sauko ko kuma ya harbe ni.

“A haka suka kwantar damu suka kwace wayoyinmu duka, sa’annan suka zabi wasu fasinjojina guda hudu da wasu fasinjojin guda 6 daka sauran motocin, suka yi awon gaba dasu zuwa cikin daji a kan babura.

“Sun bincike kayan fasinjojina suka ga kakin sojoji, inda suka tambayeni na wanene, kuma jami’in Sojan na cikinmu, amma sai na yi karya na ce musu kayan sako ne aka aike na kai Jalingo.” Inji shi.

Mai magana da yawun Yansandan jahar, David Misal ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace sun fara kokarin ceto mutanen da yan bindigan suka yi garkuwa dasu, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro da yan sa kai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel