Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Ƙona Ofishin Yan Sanda a Jihar Abia

Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Ƙona Ofishin Yan Sanda a Jihar Abia

- Wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun cinna wa ofishin yan sanda wuta a ƙaramar hukumun Bende dake jihar Abia.

- Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindigan sun kai harin ne da safiyar yau Lahadi, amma ba'a samu rasa rayuka ba saboda jami'an dake ofishin basa nan

- Wannan harin dai shine na baya-bayan nan da aka kai ofishin yan sanda tun bayan da IPOB ta ƙaddamar da jami'an tsaronta ESN a farkon shekarar nan

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun ƙona ofishin hukumar yan sanda dake kasuwar Ubani, ƙaramar hukumar Bende jihar Abia.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Jami'an Soji Sun Damƙe Mayaƙan Boko Haram 10 a Jihar Kano

Rahoton Dailytrust ya bayyana cewa yan bindigan sun mamaye ofishin ne da sanyin safiyar yau Lahadi.

Sai-dai ba'a samu rahoton rasa rayuka ba saboda jami'an dake aiki a ofishin sun bar wajen wasu yan kwanaki da suka gabata.

Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Ƙona Ofishin Yan Sanda a Jihar Abia
Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Ƙona Ofishin Yan Sanda a Jihar Abia Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Rahoton ya ƙara bayyana cewa jami'an yan sandan dake ofishin sun koma wani ofishi dake kusa da su a yankin TradeMoore.

KARANTA ANAN: An Kashe Jami’in Dan Sanda, An Kama Yan Shi’a 49 Bayan Sabon Zanga-zanga Da Aka Yi A Abuja

Wannan shine hari na baya-bayannan da aka kaiwa ofishin yan sanda tun bayan da ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biyafara (IPOB) ta kaddamar da jami'anta.

An kashe jami'an tsaro da dama tun bayan kaddamar da waɗannan jami'ai da ta saka wa suna ESN.

Jami'an yan sanda na fuskantar ƙalubalen kai musu hare-hare da ƙona kayayyakin aikinsu ko kuma ofisoshin su musamman a yankin kuduancin ƙasar nan.

A wani labarin kuma Gwamnatin Tarayya Ta Yaba da Aikin NYSC, Tace Aikin Yayi Fice Wajen Haɗa Kan Yan Najeriya

Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, yace ya zama wajibi mu cigaba da nuna goyon bayan mu ga shirin bautar ƙasa na NYSC domin yanzun shine yayi zarra wajen haɗa kan yan Najeriya.

Ministan ya ƙara da cewa, duk wata gwamnati ko ƙasa dake son tayi nasara kuma ta samar da shuwagabanni nagari, dole ta saka hanun jarinta wajen inganta rayuwar matasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel