Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa Ya Nuna Sabbin Motoci 2 Masu Tsada Wanda Kudinsu Ya Kai Naira Miliyan 300
- Ahmed Musa shine kyaftin din Super Eagles na Najeriya
- Tsohon tauraron dan wasan na Leceister City a yanzu haka yana taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars
- Musa na daya daga cikin manyan ‘yan wasan da soyayyarsu ga motoci masu tsada ba ta san iyaka ba
Ahmed Musa wanda shi ne kyaftin na Super Eagles na Najeriya ya bukaci abokai, magoya baya da abokan hulda da su yi imani da kansu yana mai cewa yin hakan zai taimaka matuka.
Tauraron dan wasan na Kano Pillars yayi wannan bayani ne yayin da yake tsaye a gaban garejinsa inda ake iya ganin motoci masu tsada guda biyu.
Ko shakka babu game da cewa Ahmed Musa na ɗaya daga cikin yan wasan Najeriya masu arziki duba da kuɗin da ɗan wasan gaban ya samu tun lokacin da ya fara harkar ƙwallon ƙafa.
KU KARANTA KUMA: Rundunar Soji Ta Tabbatar da Kamun Wasu Yan Kungiyar Boko Haram a Kano
Duk da tarin kudin da yake samawa kansa da iyalinsa, Ahmed Musa yana kuma bayar da gudummawa ga ci gaban al'umma gaba daya.
Tsohon tauraron dan wasan na Leicester City ya gina cibiyar wasanni a jihar Kano da Kaduna kuma wadannan gine-ginen guda biyu suna daya daga cikin mafi kyawu a Afirka.
KU KARANTA KUMA: Karya Ne El-Rufai Bai Taba Cewa Buhari Bai Cancanci Shugabancin Najeriya Ba – Gwamnatin Kaduna
Ana iya gano motocin G Wagon da Range Rover na miliyoyin Naira a bayan Ahmed Musa yayin da yake aika saƙonsa ga masoya da abokansa.
Bayan shafe shekaru da yawa a kasashen Turai da Asiya, Ahmed Musa a kwanan nan ya dawo gasar Lig ta Najeriya kuma zai buga wa kungiyar Kano Pillars wasa a bana.
Kano Pillars wacce ke matsayi na biyu a kan teburin NPFL a yanzu za ta kara da Warri Wolves ranar Lahadi, 9 ga Mayu, amma Ahmed Musa ba zai buga wasan ba.
Tun bayan komawarsa Kano Pillars, Ahmed Musa ya kasance yana karawa abokan wasansa karfin gwiwa saboda a yanzu sun yi amannar cewa zasu iya lashe kambun NPFL a wannan karon.
A wani labarin, mun ji cewa sabon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Ahmed Musa a jiya Alhamis, ya bayar da gudummawar naira miliyan biyu ga makarantar sakandare ta sojoji ta Bukavu da ke Kano don gina masallaci.
Kyaftin din na Super Eagles ya bayar da gudummawar ne lokacin da ya ziyarci makarantar bayan kammala atisayen ranar Alhamis.
Ya kuma yi alkawarin samar da kayan kujeru a wasu daga cikin azuzuwan domin magance matsalar karancin kujeru.
Asali: Legit.ng