Rokan China da ake tsoron zai dira Abuja ya sauka cikin Tekun Indiya

Rokan China da ake tsoron zai dira Abuja ya sauka cikin Tekun Indiya

- Rokan da kasar Sin ta harba sararin samaniya ya dawo duniya ranar Lahadi

- Masana sun yi hasashen wasu biranen da ake tsoron rokan zai iya fadowa

- Babu wanda ya ji rauni ko ya rasa rayuwarsa sakamakon fadowar rokan

Rokan da kasar Sin ta harba sararin samaniya a Afrilun 2021 ya dawo duniya yau Lahadi 9 ga Mayu cikin tekun Indiya kuma ya kama da wuta.

Rokan wanda ya bace cikin sararin samaniya ya tayar da hankalin mutane saboda rashin sanin inda zai iya sauka.

Hukumar sararin samaniyar kasar SIN (CMSA) a jawabin da ta saki ta bayyana cewa Rokan mai suna Long March 5B ya dawo duniya misalin karfe 10:24 na safe (03:24 agogon Najeriya).

"Yawancin sassan rokan sun kone yayinda ya diro, kuma ya dira ne cikin ruwa ma'aunin digiri 2.56 Latitude da digiri 72.47 Longitude," hukumar tace.

Hukumar Sojin sararin samaniyar Amurka ta tabbatar da wannan abu inda tace ya sauka a yankin Larabawa amma bata sani ko cikin ruwa ko a kasa ya fadi ba.

"A yanzu dai bamu san takamammen inda ya sauka ba kuma bamu san irin illan da yayi ba, kuma hukumar Sojin sararin samaniyar Amurka ba zata saki bayani kai ba," jawabin yace.

KU KARANTA: Ba zai yiwu a ga wata ranar Talata a Najeriya ba, amma dai a duba: Kwamitin duban wata

Rokan China da ake tsoron zai dira Abuja ya sauka cikin Tekun Indiya
Rokan China da ake tsoron zai dira Abuja ya sauka cikin Tekun Indiya
Asali: Getty Images

DUBA NAN: Zargin Badakalar N165bn: Ainihin dalilin da ya sa Buhari ya dakatad da Hadiza Bala Usman

Jiya mun kawo muku cewa masana Kimiya sun bayyana cewa Najeriya na cikin jerin kasashen ake sa ran rokan zai fado.

Biranen da akayi hasashen sun hada da; New York, Los Angeles, Madrid, Rio de Janeiro, Beijing, da birnin tarayyar Abuja.

Masana sun ba bakon abu bane sassan roka ya fado duniya, wannan ya zama abin damuwa saboda rokan ya bace ne kuma ba'a san inda zai fado ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel