Turkiyya: Kasar Musulunci Ta Yi Kazamin Makamin da zai Iya Zuwa Nahiyoyi
- Rahotanni sun nuna cewa kasar Turkiyya ta bayyana wani kazamin makami mai linzami da zai iya kai wa nahiyoyi daban-daban a duniya
- Bincike ya nuna cewa idan aka harba hatsabibin makamin zai iya kai nisan mil sama da 3,000, inda aka ce zai iya kai wa Turai, Afirka da Asiya
- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Gabas ta Tsakiya ke cigaba da zama cikin dar-dar tun bayan hare-haren da Isra'ila ta kaddamar a Iran
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Turkey - Gwamnatin kasar Turkiyya ta bayyana samfurin makami mai linzami mai iya kai wa nahiyoyi daban-daban a fadin duniya.
Ta yi haka ne a matsayin wani bangare na kokarinta na dogaro da kai da kuma neman zama babbar kasa a bangaren tsaro a Gabas ta Tsakiya da kuma tsakanin kawayenta na NATO.

Kara karanta wannan
Matar da APC ta tsaida takara a Katsina ta fara fuskantar cikas daga malaman Musulunci

Source: Getty Images
Al Jazeera ta ce an nuna makamin mai suna Yildirimhan, ma’ana “walƙiya” a harshen Turkiyya, wanda cibiyar bincike da kirkire-kirkire ta Ma’aikatar Tsaro ta kirkira a bikin baje kolin tsaro da sararin samaniya na SAHA 2026.
Bayani game da makamin Turkiyya
Rahoton da tashar TRT ta wallafa ya nuna cewa makamin Yildirimhan na da nisan zangon kai hari da zai kai kilomita 6,000 (mil 3,278).
A cewar wata cibiya a Amurka, ana daukar makamai masu zangon kai hari sama da kilomita 5,500 (kimanin mil 3,418) a matsayin masu dogon zango daga nahiya zuwa nahiya (ICBMs).
Idan aka harba shi daga Turkiyya, Yildirimhan zai iya kai hari kan wurare a Turai, Afirka da Asiya kuma yana dauke da rokoki guda hudu.
Jawabin ministan tsraon Turkiyya
Da yake jawabi a wajen baje kolin da aka gudanar a Istanbul na kasar Turkiyya, Ministan Tsaro Yasar Guler ya ce:
“A wannan zamani da matsalar tattalin arziki ta zama kalubale a duniya, Turkiyya za ta ba kawayenta tabbacin a kan fasaha da tattalin arzikin tsaro mai dorewa.”
Bayanin masana kan makamin
Masana sun bayyana cewa kaddamar da makami mai dogon zango na Turkiyya yana da muhimmanci saboda dalilai da dama.
Shugaban sashen bincike na wata cibiya a Amurka, Ozgur Unluhisarcikli, ya shaida cewa:
“A ganina, Turkiyya ba ta bukatar ICBMs domin dakile wata barazanar tsaro ta gaggawa da take fuskanta. Saboda haka, ba ICBM din kansa ba ne ke da muhimmanci ga Turkiyya, illa karfin iya kera shi.”
Wani masani kan tsaro da harkokin makamai da ke Istanbul, Burak Yildirim ya ce tsarin kirkirar ICBM yana da muhimmanci kai tsaye ga kokarin Turkiyya na harba kayayyakin sararin samaniya.

Source: Getty Images
Rahotanni sun nuna cewa bayyanar sabon makamin na zuwa ne a lokacin da ake fama da tsananin tashin hankali a Gabas ta Tsakiya.
Amurka ta kai hari kasar Iran
A wani rahoton, kun ji cewa lamura na cigaba da dagulewa a Gabas ta Tsakiya duk da tsagaita wuta da aka yi tsakanin Amurka da Iran.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa sun kai hari kasar Iran bayan wani farmaki da ya ce an kai hari kan jirgin ruwansu.
Sai dai duk da harin da aka kai, shugaba Donald Trump ya sanar da cewa yarjejeniyar da suka yi game da tsagaita wutar tana nan daram.
Asali: Legit.ng

