Buhari zai yi bikin sallah a fadar Aso Rock, yace baya bukatar gaisuwar sallah

Buhari zai yi bikin sallah a fadar Aso Rock, yace baya bukatar gaisuwar sallah

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa zai yi sallar idi a fadarsa dake Aso Rock a Abuja

- Ya bukaci shugabannin addinai, al'umma da na yankuna da su sha zamansu lafiya ba tare da sun kai masa gaisuwa ba

- Yace ya ukaci hakan ne sakamakon muguwar annobar korona da ta zama ruwan dare dama duniya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da haramta kai masa gaisuwar sallah daga shugabannin addinai, yankuna da na siyasa kuma yace a fadarsa ta Aso Rock zai yi sallar Idi.

A wata takarda da shugaban kasa ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya wallafa a Facebook, ya hori shugabanni da su zauna gidajensu don yin bikin sallah sakamakon annobar korona.

Kamar yadda takardar ta bayyana, "Yayin da Musulmin Najeriya da sauran na duniya suke hango bikin sallah, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin karanta shagulgula saboda cutar korona da ta addabi duniya.

KU KARANTA: 'Yan ta'addan ISWAP sun tarwatsa sansanin soji a jihar Borno

Buhari zai yi bikin sallah a fadar Aso Rock, yace baya bukatar gaisuwar sallah
Buhari zai yi bikin sallah a fadar Aso Rock, yace baya bukatar gaisuwar sallah. Hoto daga @daily_trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Melaye: Buhari ya fito yayi mana magana, ba Garba Shehu ko Adesina muka zaba ba

"A saboda haka, shugaban kasa, iyalansa, hadimansa, masu makamai da shugabannin tsaronsa wadanda suke Abuja zasu yi sallar Idi a fadarsa. Lokacin sallar Idi shine 9 na safe.

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari na mika godiya ga malamai addinin Islama da Kirista kuma yana bukatar su cigaba da yi wa kasar nan da mutanenta addu'a."

Shugaban kasan yayi amfani da wannan damar wurin mika ta'aziyyarsa ga wadanda suka rasa 'yan uwansu a sassan kasar nan.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga dukkan shugabannin yankuna da su yi magana da matasa tare da jan musu kunne a kan kada a yi amfani da su wurin tada tarzoma.

A wani labari na daban, duk da shigar 'yan sanda tashin hankalin dake faruwa a yankin Mile 12 a jihar Legas, kungiyoyin dake fada sun cigaba da tada zaune tsaye.

Premium Times ta ruwaito yadda 'yan sanda suka cafke mutum 45 da ake zargi bayan rikicin ya barke a yankin Mile 12.

'Yan sandan sun ce lamarin ya faru ne bayan zargin wani Alhaji Alidu da aka yi da batanci ga Annabi Muhammad. Shine kwamandan kungiyar 'yan sintirin yankin Gengere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel