An karya alkawari, Malamai suna bin Gwamnatin Buhari bashin albashin watanni 15 inji ASUU

An karya alkawari, Malamai suna bin Gwamnatin Buhari bashin albashin watanni 15 inji ASUU

- Kungiyar ASUU ta bayyana irin tulin kudin ta da su ke hannun Gwamnati

- Shugaban ASUU ya ce an yi fiye da watanni 15, ba a biya wasu Malamai ba

- Biodun Ogunyemi yake cewa Gwamnati ta saba MOU din da aka sa hannu

Jaridar The Nation ta rahoto cewa wasu cikin malaman jami’a a Najeriya suna bin gwamnatin tarayya bashin albashin watanni 15 zuwa 16.

Kungiyar ASUU ta bayyana cewa wasu daga cikin malaman da suke karantarwa a jami’o dabam-dabam sun shafe watanni ba tare da albashi ba.

ASUU ta ce har zuwa jiya, gwamnatin tarayya ta gagara tabbatar da cikakkun bayanan da ake bukata a game da hakkokin wadannan malamai.

KU KARANTA: “Babu tanadin da aka yi domin maganin cutar COVID-19 a Jami'o'i”

Kungiyar malaman jami’o’in ta zargi ofishin babban akawun gwamnati na kasa, da kitsa wannan aiki da nufin bata wa malamai rai saboda IPPIS.

Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya ce kin biyan wasu malamai albashinsu, ya saba wa yarjejeniyar da aka sa wa hannu a 2020.

“Gwamnati a na ta bangaren, za ta iya cewa ta biya duka bashin albashin, amma ba zai yiwu ku ce kun biya kudi, a lokacin da wasu suke bin bashi ba.”

“Har yanzu ‘yan kungiyarmu na bin bashi. Mu na bibiyar kudin; ana biya ne gutsun-gutsun, amma har yau akwai wasu ‘ya ‘yanmu da ba a biya su ba.”

KU KARANTA: Dole sai an komawa Allah kafin a samu zaman lafiya – Yombe

An karya alkawari, Malamai suna bin Gwamnatin Buhari bashin albashin watanni 15 inji ASUU
Shugabannin ASUU a taro Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

“Kai, akwai wadanda ba a biya su na tsawon watanni 15-16 ba. Wadanda su ka yi aiki a wasu jami’o’i, ba su samu kudinsu ba, ana neman kai su makura.”

Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce ana yin haka ne saboda a cusa malaman a cikin tsarin IPPIS.

Biodun Ogunyemi yake cewa da wasu malamai suka kai kuka, an sanar da su karara, ba za a ba su albashinsu ba har sai sun yi rajista da manhajar IPPIS.

A bara ne karamin ministan ilmin Najeriya, Hon. Chukwuemeka Nwajiuba, ya yi kira ga ‘yan kungiyar ASUU na malaman jami’a, su koma harkar noma.

Chukwuemeka Nwajiuba ya ce idan malaman ba za su iya aikin malanta ba, su hakura, su rungumi wata sana'ar da za ta rika kawo masu abin kashewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel