Watakila fetur ya kara tsada – Masana sun ba Buhari shawarar ya cire tallafin mai

Watakila fetur ya kara tsada – Masana sun ba Buhari shawarar ya cire tallafin mai

- Majalisar mashawarta sun yi zama na musamman a makon da ya wuce

- PEAC ta ba Shugaban kasa shawarar ya daina biyan tallafin man fetur

- An gargadi Gwamnatin Tarayya a kan tasirin hakan kan tattalin arziki

Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa majalisar PEAC mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tattalin arziki ta kawo shawarar janye tallafin fetur.

Majalisar mashawartar ta na so a daina biyan kudin tallafin man fetur, a bar farashin kasuwa ya tsaida yadda za a rika saida litar mai a gidajen mai a Najeriya.

A zaman da majalisar ta yi a ranar Juma’a, ta kawo shawarwari da-dama, daga ciki ta ce biyan kudin tallafin fetur zai kara jefa jihohin Najeriya cikin matsala.

KU KARANTA: Tallafin man fetur ya lashe N308bn cikin watanni uku

Bayan bukatar ayi watsi da tsarin da aka sake dawo da shi na biyan kudin tallafin fetur, majalisar PEAC ta yi kira ga gwamnati ta yi maza ta fara aiki da kudirin PIB.

PEAC ta ce tun da ba a sa tallafin mai a cikin kasafin kudin 2021 ba, kudin da NNPC ta ke biya domin a cike gibin farashin mai zai yi kasa da lalitar gwamnati.

Idan aka cigaba da tafiya a haka, mashawartan sun ja-kunne cewa za a maida Najeriya zuwa 2015, lokacin da ta kai sai da gwamnatin tarayya ta ba jihohi aron kudi.

Farfesa Doyin Salami da sauran ‘yan majalisarsa sun sanar da gwamnati cewa biyan tallafin mai da ake yi, ya jawo ‘yan kasuwa ba su sha’awar shiga harkar fetur.

Watakila fetur ya kara tsada – Masana sun ba Buhari shawarar ya cire tallafin mai
Majalisar PEAC a taro Hoto: @NigeriaGov
Asali: Twitter

KU KARANTA: NPA: Gwamnatin Buhari ta yi wa dokokin kasa hawan kawara

Kamar yadda takardar zaman majalisar da jaridar ta samu ya nuna, PEAC ta fadakar da gwamnati a kan cire tallafin fetur ya fi cigaba da biyan wannan kudi amfani.

Majalisar masanan ta yi ittifaki a kan tsaro ya tabarbare, ta ce hakan ya na da mummunan tasiri a kan harkar tattalin, ta yi kira ayi maganin masu tada kafar baya.

Yanzu ya rage ga shugaba Muhammadu Buhari ya duba wadannan shawarwari da aka kawo masa.

A kwanan bayan nan ne aka ji gwamnatin tarayya ta na shirye-shiryen cire tallafin mai. Gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi hakan ne nan ba da jimawa ba.

Karamin ministan mai, Timipre Sylva, shine ya bayyana haka a lokacin da ya zanta da manema labarai a wajen yaye wasu ɗalibai a jami'ar Fatakwal, a jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel