Dakarun Sojoji Sun Dakile Mummunan Harin Yan Ta'adda, Sun Tura 50 Lahira a Jihar Yobe

Dakarun Sojoji Sun Dakile Mummunan Harin Yan Ta'adda, Sun Tura 50 Lahira a Jihar Yobe

  • Dakarun sojoji sun yi nasarar dakile harin da 'yan ta'addan ISWAP suka yi yunkurin kai wa sansanin soji da ke garin Buni Gari a jihar Yobe
  • Rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai (OPHK) ta tabbatar da hakan yau Asabar, inda ta ce dakarun sojoji sun kashe 'yan ta'adda 50
  • Rahoto ya nuna cewa bayan fatattakar yan ta'adda, jiragen yaki da sojojin kasa sun sake bin sawinsu, inda aka gano karin gawarwaki 20

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai (OPHK) da ke Arewa maso Gabas ta dakile wani mummunan hari da mayaƙan ISWAP suka kai sansanin Brigade ta 27 da ke Buni Gari, jihar Yobe.

Yayin dakile wannan hari, dakarun sojojin sun yi nasarar hallaka 'yan ta'addan kungiyar ISWAP 50. Sai dai sojoji biyu sun rasa rayukansu yayin musayar wutar a daren Juma'a, 8 ga Mayu, 2027.

Kara karanta wannan

An zubar da jini bayan sojoji sun gwabza da 'yan ta'addan ISWAP a Borno

Sojoji.
Dakarun sojojin Najeriya a cikin daji a kokarin kakkabe yan ta'adda da suka addabi al'umma Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafin X yau Asabar, dauke da sa hannun kakakin rundunar OPHK, Laftanar Kanal Sani Uba.

Ya ce mayaƙan ISWAP sun kai harin ne daga wurare daban-daban a duhun dare, amma sojoji sun mayar musu da martani mai ƙarfi tare da nuna bajinta da ƙwarewa wajen kare sansanin.

Sojoji sun murƙushe mayakan ISWAP

Sanarwar ta ce mayaƙan sun fara kai hari ne daga yammacin sansanin sojin kafin daga baya su turo karin mayaƙa ta bangaren Kudu ta hanyar Ganinga Junction, sannan suka sake kai farmaki daga Kudu maso Yamma da nufin kewaye sojojin.

Sai dai jami’in ya bayyana cewa sojojin sun tsaya tsayin daka tare da amfani da dabarun yaki masu inganci da suka haddasa mummunar asara ga 'yan ta'adda.

“Akalla ’yan ta’adda 50 aka hallaka, yayin da aka kwato tarin makamai da alburusai daga hannun ragowar da suka tsere,” in ji sanarwar.

Kara karanta wannan

'Ka yi da matata, in yi da matarka,' An kama abokai da ke musayar matansu a Bauchi

Jiragen yaki sun taka rawa a lamarin

Rundunar ta ce bangaren jiragen sama na OPHK ya bayar da gudunmawa ta hanyar sa ido da tattara bayanan sirri domin gano inda mayaƙan suke.

A cewar sanarwar, an kai hare-haren sama kan wuraren da aka gano mayaƙan da kuma wadanda ke guduwa, lamarin da ya kara hallaka wasu ’yan ta’adda 20.

Bincike daga jami’an leƙen asiri ya kuma nuna cewa an ga karin gawarwakin mayaƙan a yankunan Gashua, Azare da Kamuya yayin da suke tserewa.

Yobe.
Taswirar jihar Yobe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rundunar ta bayyana cewa an kwato makamai da kayan yaki da dama daga hannun mayaƙan, ciki har da bindigogi kirar AK-47 guda takwas, manyan bindigogi guda biyu kirar GPMG, bindigogin roka guda biyu da sauran kayayyakin fashewa.

Sojoji sun gano masana'antun kera makamai

A wani labarin, kun ji cewa sojojin Najeriya sun samu nasarar gano wasu wurare da ake kera makamai a cikin jihar Filato da ke fama da rikicin kabilanci.

Sojojin sun kuma kama wasu mutane biyar da ake zargi tare da ƙwace tarin makamai da harsasai daga wadannan wuraren da suka bankado.

Kayayyakin da aka ƙwace sun haɗa da bindigun AK-47 guda tara da aka ƙera, bindiga ƙirar gida guda ɗaya da mujallu huɗu na AK-47 marasa harsasai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262