Musulmi Ya Sake Ɗarewa Kujerar Magajin Garin Landan Bayan Lashe Zaɓe

Musulmi Ya Sake Ɗarewa Kujerar Magajin Garin Landan Bayan Lashe Zaɓe

- Musulmi na farko da ya taɓa lashe zaɓen magajin garin Landan, Sadiq Khan, ya sake komawa kan kujerar sa a karo na biyu bayan kammala Zaɓe

- Khan ya sake samun nasara ƙarƙashin jam'iyyar hamayya ta Labour da kashi 55.2% yayin da babban abokin takararsa keda kashi 44.8%

- Sadiq ya nuna tsantsar farin cikinsa bisa amincewar da mutanen Landan suka sake yimasa na ya cigaba da jagorantar su, yayi alƙawarin bazai kunyata su ba

Sadiq Khan, musulmi na farko da ya taɓa riƙe muƙamin magajin garin Landan ya sake komawa kujerarsa a karo na biyu.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Jami'an Soji Sun Damƙe Mayaƙan Boko Haram 10 a Jihar Kano

Rahoton BBC ya bayyana cewa Sadiq Khan ya sake komawa kan kujerar sa ne bayan doke abokin takararsa, Shaun Bailey, na jam'iyyar Conservative.

Khan ya samu nasara da kashi 55.2% yayin da ya kayar da abokin takarar sa Baily wanda ya samu 44.8% a zagaye na biyu na zaɓen da aka gudanar.

Musulmi Ya Sake Ɗarewa Kujerar Magajin Garin Landan Bayan Lashe Zaɓe
Musulmi Ya Sake Ɗarewa Kujerar Magajin Garin Landan Bayan Lashe Zaɓe Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Sadiq Khan wanda tsohon dan majalisa ne, shine musulmi na farko da ya fara lashe zaɓen magajin garin Landan a shekarar 2016, ya kuma sake komawa kujerarsa a karo na biyu.

KARANTA ANAN: Gwamnatin Tarayya Ta Yaba da Aikin NYSC, Tace Aikin Yayi Fice Wajen Haɗa Kan Yan Najeriya

Khan yace: "Nayi matuƙar farin ciki da irin amincewar da mutanen Landan suka mun na in sake jagorantar birnin da yafi kowanne a faɗin ƙasa."

"Na yi alƙawarin zan yi amfani da kowacce irin dama da nike da ita wajen kawo kyakkyawan cigaba a Landan bayan wannan annobar da muke fama da ita ta shuɗe."

A wani Labarin kuma Aljanu Biliyan 3 su ka karbi Darikar Tijjaniya a Duniya inji Sheikh Dahiru Bauchi

Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi wata magana wanda ta ba dinbin mabiyansa da sauran al’umma mamaki.

Shehin malamin ya bayyana cewa akwai wasu kebantattun mutane da su ke iya sadu wa da aljanu. Ya ce ya na daga cikin masu mu’amala da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: