NDLEA Ta Bankado Masu Safarar Miyagun Kwayoyi Ta Yanar Gizo, Ta Kama 5 a Abuja

NDLEA Ta Bankado Masu Safarar Miyagun Kwayoyi Ta Yanar Gizo, Ta Kama 5 a Abuja

- Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta bankaɗo wasu gurɓatattun mutane dake safarar ƙwayoyi a yanar gizo

- A binciken da NDLEA tayi ta samu nasarar cafke mutane biyar a babban birnin tarayya Abuja ta hanyar ɗana musu tarko da siyan kayan su a yanar gizo

- Waɗanda aka kama ɗin sun amsa laifin su, kuma sun bayyana yadda suke gudanar da kasuwancin tare da kwastomominsu a yanar gizo

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA, ta bankaɗo wasu masu safarar miyagun ƙwayoyi ta yanar gizo waɗanda ke siyarwa mazauna Abuja dama waje ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta.

KARANTA ANAN: Musulmi Ya Sake Ɗarewa Kujerar Magajin Garin Landan Bayan Lashe Zaɓe

A sakamakon haka ne, jami'an hukumar NDLEA reshen Abuja suka sami nasarar cafke tawagar mutane biyar dake gudanar da wannan ɗanyen aiki.

Hukumar NDLEA ta sanar da samun wannan nasarar ne a wani rubutu data yi a shafinta na kafar sada zumunta Tuwita.

NDLEA ta bankado masu safarar miyagun kwayoyi ta yanar gizo, ta kama 5 a Abuja
NDLEA ta bankado masu safarar miyagun kwayoyi ta yanar gizo, ta kama 5 a Abuja Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

Waɗanda aka kama da zargin safarar miyagun ƙwayoyin ta yanar gizo sun haɗa da; Queen Nvene, Collins Ozoemena, Samson Peter, Chika Nvene da kuma Habila Musa.

Tawagar waɗanda aka kama ɗin sun ƙware wajen samar da haramtattun ƙwayoyi a cikin kayan ciye-ciye irin su kek da makamantanshi; kuma suna kasuwanci da siyar da su ta yanar gizo.

Suna amfani da kafafen sada zumunta na Tuwita da kuma Instagram wajen gudanar da kasuwancin su.

Yayin da Queen Nvene, wacce ta kammala digirinta na farko a fannin kasuwanci, take samar da kwayoyin kukis da kek kuma ta siyar dasu a kafar sada zumunta Instagram, shi kuma Collins Ozoemena yana siyar da dukkan haramtattun ƙwayoyi ta yanar gizo.

A ɗaya ɓangaren kuma Samson Peter shine manajan kamfanin SK Express Courier, shike sarrafa mashina da kuma waɗanda ake aike su kai kwayoyin da aka siya daga Collins da kuma kokis, kek daga Queen da Chika.

Dukkan su mambobin tawaga ɗaya ne da suke aiki daga ɓangarori daban-daban na Abuja a yanar gizo.

NDLEA ta cafke waɗannan mutanen ne ta hanyar siyan kayayyakin su a yanar gizo da wasu daga cikin jami'anta suka yi kuma aka aiko ɗan aiken kamfanin ya kawo musu kwayoyin kek ɗin kamar yadda suka buƙata a lokuta daban-daban.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Ƙona Ofishin Yan Sanda a Jihar Abia

A jawabin da kwamandan NDLEA reshen Abuja, Muhammed Malami, yayi yace:

"Bayan bibiyar wuraren da suke gudanar da ayyukansu a Gudu, Kubwa, Lokogoma, Apo da kuma Damangazo duk a Abuja, an kwato kwayoyi masu illatarwa da dama."

"Abubuwan da aka ƙwato sun haɗa da; kek ɗin da aka haɗa da ƙwayoyi 55, kayayyakin haɗa kek, mashin ɗin hawa, wayoyin hannu, Na'ura mai ƙwaƙwalwa guda biyu, da sauransu."

A yayin bincike, mutanen da ake zargin sun amsa laifinsu kuma sunce suna da babban dandali wanda suke gudanar da kasuwanci tsakaninsu da kwastomominsu a kafar sada zumunta.

Mutanen sun ƙara da cewa suna da kwastomomi waɗanda ke sayen kayayyakin su a ciki da wajen babban birnin tarayya Abuja.

Hakanan kuma sunce suna amfani da manajan kamfanin SK Express wajen isar da kayansu ga kwastomominsu, kuma sun tabbatar da sun ɗauki tsawon shekaru uku suna gudanar da wannan aikin.

A ɗayan bangaren kuma, jami'an NDLEA reshen jihar Ondo sun ƙwace kilo 60 na ƙwayar kannabis biyo bayan amfani da fasahar zamani da suka yi.

Jami'an sun damke, Emmanuel Utaji, ɗan shekara 29 a layin Metado Akure, ƙaramar hukumar Akure ta kudu.

Muƙaddashi kwamandan NDLEA na jihar, Callyns Alimona, ya bayyana cewa jami'ai sun mamaye maɓoyarsa ne da misalin ƙarfe 9:45 na dare lokacin da ake kokarin fitar dashi daga cikin jihar.

A makamancin irin wannan ne, jami'an NDLEA na jihar Rivers suka cafke, Sanusi Abdullahi, wanda ake zargi da safarar ƙwayoyi a ƙauyen Iroko.

Da yake martani kan nasarar da hukumar ta samu, shugaban NDLEA na ƙasa, janar Muhamed Buba Marwa, ya jinjinawa jami'an hukumar na FCT, Ondo da Rivers bisa wannan namijin ƙoƙarin da suka yi.

Marwa yace: "Nayi matuƙar farin ciki da wannan aikin da jami'an mu na FCT sukayi, inda suka bankaɗo masu safarar miyagun ƙwayoyi a yanar gizo da suka shafe shekaru suna gurbata mutane a ƙasar nan, ina jinjina a garesu.

"Sanann ina jinjina ga takwarorin su na jihar Ondo da Rivers bisa nasarar da suka samu a baya-bayan nan"

A wani labarin kuma Jami'an Soji Sun Damƙe Mayaƙan Boko Haram 10 a Jihar Kano

Sojoji sun yi ram da wasu mutane da ake zargin mayaƙan ƙungiyar ta'addaci ta Boko Haram ne a cikin garin Kano ranar Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla mutane 10 ne suka shiga hannu lokacin da suka yi ƙoƙarin kai hari wani masallaci a yankin Hotoro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel