APC Ta Tantance Abba, Ya Zama Dan Takarar Gwamna Tilo a Kano
- Jam’iyya.mai mulki ta APC ta tantance Gwamna Abba Kabir Yusuf domin neman wa’adi na biyu a zaɓen 2027
- Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nantawe Yilwada, ya ce gwamnan ya cika dukkamin sharudan takara da ake buƙata
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alƙawarin ci gaba da kawo ci gaba da haɗin kai a jihar Kano kamar yadda ya fara a yanzu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jam’iyyar APC ta amince da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, domin tsayawa takarar wa’adi na biyu a zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a shekarar 2027.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu ranar Juma’a, 7 ga watan Mayu, 2026.

Source: Facebook
Sanarwar da Sanusi Bature ya wallafa a shafinsa na Facebook ta bayyana cewa tantancewar ta biyo bayan nasarar da gwamnan ya samu a gaban kwamitin ayyuka na ƙasa na APC bayan ya miƙa fam ɗin tsayawa takara da na tantancewa.
APC ta amince da takarar Abba
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nantawe Yilwada, wanda ya jagoranci kwamitin tantancewar a gidan gwamnatin gwamnan jihar Filato, ya ce jam’iyyar ta tabbatar da cewa Gwamna Yusuf ya cika dukkanin sharuddan da ake buƙata domin neman wa’adi na biyu.
Ya ce bayan kammala aikin tantancewar, an bayyana Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya rage shi kaɗai a halin yanzu wajen neman tikitin takarar gwamna na APC a jihar Kano gabanin zaɓen 2027.
Sanarwar ta ƙara da cewa shugabannin jam’iyyar sun yaba da yadda gwamnan ya gudanar da harkokin mulki tare da nuna gamsuwa da irin goyon bayan da yake samu daga magoya bayan jam’iyyar a jihar Kano
Gwamnan Kano ya sha alwashi
Da yake jawabi bayan tantancewar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode wa shugabannin APC bisa irin amincewa da goyon bayan da suka nuna masa.
Ya ce zai ci gaba da aiki domin samar da ribar dimokuraɗiyya ga al’ummar jihar Kano tare da ɗorewa kan manufofin da za su inganta zaman lafiya, bunƙasar tattalin arziki da ci gaba mai amfani ga kowa.

Source: Facebook
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da suka shafi matasa, mata da sauran al’umma domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a jihar.
Har ila yau, ya yi kira ga ‘ya’yan APC da magoya bayan jam’iyyar da su ci gaba da haɗa kai tare da yin aiki tare domin ganin an samu nasarar jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027.
Sanarwar ta ƙara da cewa APC na da kwarin gwiwar cewa haɗin kai da goyon bayan ƴaƴanta za su taimaka wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar a Kano a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan
NDC: Kwankwaso ya mika sakon kar ta kwana gabanin rufe rajistar jam'iyyu a Najeriya
Gwamnan Kano ya kai dan Abuja
A baya, kun samu labarin cewa gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya miƙa takardar tsayawa takarar gwamna ta 2027 ga uwar jam'iyya mai mulki ta APC.
Manyan jagororin Kano daga ciki har da Sanata Ibrahim Shekarau da Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin sun raka shi kai fam babban birnin tarayya.
Gwamnan ya yi alƙawarin ƙara zuba kudi wajen gina tituna, samar da ilimi, lafiya da bunƙasa karkara kamar yadda ya fara ayyukan samar da ci gaban Kano.
Asali: Legit.ng

