Shugabannin jam’iyyar APC sun sallama, sun kai kukan matsalar tsaro gaban Allah

Shugabannin jam’iyyar APC sun sallama, sun kai kukan matsalar tsaro gaban Allah

- Shugaban Matasan APC ya sa an gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya

- Alhaji Sadiq Sa’ad Fakai da wasu Bayin Allah sun yi zaman addu’o’i a Kebbi

- Mataimakin Gwamnan Kebbi ya yi kira ga al’umma su komawa Allah SWT

Rahotanni daga hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN, sun tabbatar da cewa an gudanar da addu’o’i na musamman domin samun tsaro a Najeriya.

Wasu matasan jam’iyyar APC a yankin Arewa maso yammacin Najeriya sun shirya addu’o’i da nufin a samu zaman lafiya da hadin kai a fadin kasar nan.

Wadannan matasa sun yi wadannan addu’o’i ne a ranar Lahadi, 9 ga watan Mayu, 2021, a masallacin Mai martaba Sarkin Gwandu da ke jihar Kebbi.

KU KARANTA: Ba mu goyon bayan a rika biyan kudin fansa - ACF

Matasan sun dauki wannan mataki ne bayan ganin yadda ake fama da hare-haren ‘yan bindiga, ta’adin Boko Haram, da barnar masu garkuwa da mutane.

Shugaban matsan jam’iyyar APC na reshen Arewa maso yamma, Alhaji Sadiq Sa’ad Fakai, ya sa aka jagoranci wannan addu’o’i da aka gabatar a Birnin Kebbi.

Alhaji Sadiq Sa’ad Fakai ya roki Ubangiji ya kintsa wa Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran shugabanni hikimar jagorancin da suke kai.

Har ila yau, matasan na APC sun yi wa wadanda su ka rasa ‘yanuwa da abokan arziki a sanadiyyar hare-haren ‘yan bindiga addu’ar Ubangiji ya jikansu.

KU KARANTA: PEAC ta ba Shugaban kasa shawarwar ya yi maganin 'Yan bindiga

Shugabannin jam’iyyar APC sun sallama, sun kai kukan matsalar tsaro gaban Allah
Shugaban kasa ya na sallar idi a gida Hoto: www.tribuneonlineng.com

Bayan an kammala addu’o’in, mataimakin gwamnan Kebbi, Alhaji Sama’ila Yombe, ya yi jawabi, ya ce dole mutanen kasar nan su komawa Allah madaukaki.

Mai girma Sama’ila Yombe ya yi kira ga jama’a su tuba, su roki gafarar Ubangiji domin a shawo kan matsalar rashin tsaron da ya ki ci, ya ki cinyewa har yanzu.

Manyan malaman da su ka halarci zaman sun hada da; Malam Modibbo Gwandu, Malam Nata’ala Birnin Kebbi da Malam Lawali Birnin Kebbi da dai sauransu.

Kwanaki Sheikh Dahiru Bauchi ya ce akwai Aljanu biliyan uku a cikin darikar Tijjaniya, kuma ana duba yiwuwar amfani da Aljanun nan wajen maganin miyagu.

Shehin malami ya ce akwai yiwuwar zai nemi Aljanu su sa hannu a rika kubutar da ‘Yan Tijjaniya daga hannun ‘Yan bindiga da 'Yan ta'addan Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel