Da Duminsa: ’Yan Bindiga Sun Kashe Jigo a Kaduna, Matarsa da Sirikarsa

Da Duminsa: ’Yan Bindiga Sun Kashe Jigo a Kaduna, Matarsa da Sirikarsa

- Wasu yan bindiga sun kashe jigo a garin Golkofa dake ƙaramar hukumar Jema'a a jihar Kaduna kamar yadda kwamishina tsaron jihar ya sanar

- Yan bindigan sun harbi mutumin tare da matarsa da sirikarsa a harin da suka kai musu har gida, inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsu

- Rahoton ya bayyana cewa mutum ɗaya ne ya tsira kuma shima yan bindigan sun ji masa munanan raunuka

Wasu yan bindiga sun sheƙe wani jigo, Christopher Madaki, tare da matarsa da kuma sirikarsa a garin Golkofa ƙaramar hukumar Jema'a jihar Kaduna.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Ƙona Ofishin Yan Sanda a Jihar Abia

Kwamishinan tsaron cikin gida, Mr. Samuel Aruwan, shine ya sanar da haka a wani saƙo.

Kwamishina yace:

"Hukumar yan sanda ta jihar Kaduna da hedkwatar tsaro, sun aikewa gwamnatin jihar Kaduna rahoton kisan mutane uku yan asalin jihar."

"A bayanan da muka samu bayan faruwar lamarin, yan bindigan sun farmaki gidan Christopher Madaki, jigo a garin Golkofa karamar hukumar Jema'a suka harbe shi, tare da matarsa da kuma matar ɗansa (sirikarsa)."

"Daga baya aka tabbatar da mutuwar su, yayin da ɗansa, Clement Musa Madaki, ya tsira da muggan raunuka."

Da Duminsa: ’Yan Bindiga Sun Kashe Jigo a Kaduna, Matarsa da Sirikarsa
Da Duminsa: ’Yan Bindiga Sun Kashe Jigo a Kaduna, Matarsa da Sirikarsa Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

KARANTA ANAN: Musulmi Ya Sake Ɗarewa Kujerar Magajin Garin Landan Bayan Lashe Zaɓe

"An bayyana sunan matar mutumin da, Mary Christopher Madaki, da kuma sirikarsa, Alice Musa." inji Aruwan.

Hakanan kuma, Mr. Aruwan ya ƙara da cewa rundunar soji ta 'Operation Safe Haven' sun sami wani rahoto na batan wani mutumi mai suna, Ngode Patrick Kambai, a ƙauyen Mabuhu ƙaramar hukumar Zangon Kataf.

A wani labarin kuma Ortom Ya Yiwa El-Rufai Wankin Babban Bargo, Ya Ce Yana Daya Daga Cikin Makiyan Najeriya Na Hakika

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya bayyana takwaransa na Kaduna a matsayin daya daga cikin makiyan Najeriya.

Gwamnan na Benuwai yana mayar da martani ne ga wata sanarwa da aka alakanta da El-Rufai wanda ya zargi Ortom da amfani da rashin tsaro a jiharsa wajen kai hari ga gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262