An Saka Sunan El Rufai, Ganduje da Malami kan Zargin Kisan Dadiyata

An Saka Sunan El Rufai, Ganduje da Malami kan Zargin Kisan Dadiyata

  • Dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore ya bukaci a gayyaci wasu manya a Najeriya domin amsa tambayoyi kan batan Abubakar Idris watau Dadiyata
  • Sowore ya nuna rashin amincewa da binciken rundunar ‘yan sanda, yana mai neman a kafa kwamitin bincike na shari’a mai zaman kansa
  • Dadiyata ya bace tun kusan shekaru bakwai bayan wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun sace shi daga gidansa da ke Kaduna

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Dan gwagwarmayar kare hakkin bil’adama, Omoyele Sowore, ya bukaci a gayyatar wasu tsofaffin gwamnoni dan zargin kisan Abubakar Idris watau Dadiyata.

Sowore ya ce ya kamata a gayyaci Nasir El-Rufai da Abdullahi Umar Ganduje domin yi musu tambayoyi kan batan Abubakar Dadiyata.

An bukaci binciken Ganduje, El-Rufai game da Dadiyata
Abdullahi Ganduje (hagu), da Abubakar Idris, Dadiyata (tsakiya), da Malam Nasir El-Rufai (dama). Hoto: Hoto: @elrufai, @GovUmarGandujee, @ADCngcoalition (X).
Source: UGC

Legit Hausa ta samu wannan bukata ta Sowore a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Asabar 9 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta gano kuskure, ta yi gyara a sunan da ake kiran Shugaba Bola Tinubu

An zargi Ganduja, El-Rufai kan batan Dadiyata

Sowore ya bayyana cewa bai yarda rundunar ‘yan sandan Najeriya za ta gudanar da sahihin bincike ba musamman idan lamarin ya shafi manyan ‘yan siyasa ba.

Ya kuma nemi a gayyaci tsohon darakta janar na DSS, Yusuf Bichi da tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami SAN, domin bayar da bayani kan lamarin.

Ya ce saboda haka akwai bukatar a kafa kwamitin bincike na shari’a wanda zai gayyaci tsofaffin jami’an gwamnati da jami’an tsaro domin gano gaskiyar abin da ya faru da Dadiyata.

Ya ce:

"Bari na fayyace komai, ban yarda da bangaren binciken rundunar yan sanda ba da keda alhakin gano dalilin batan Dadiyata da zargin kashe shi da ake yi."

Ya kara da cewa dole ne a gayyaci El-Rufai, Ganduje, Yusuf Bichi, tsohon sufeto janar na ‘yan sanda da kuma Malami saboda zargin suna da hannu a lamarin.

Sowore na zargin Ganduje, El-Rufai game da Dadiyata
Dan gwagwarmaya kuma lauya a Najeriya, Omoyele Sowore.
Source: Facebook

Dadiyata: Matakin da yan sanda suka dauka

Rahotanni sun bayyana cewa Dadiyata, mai sharhi a kafafen sada zumunta da ke Kaduna, ya bace ne bayan wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun sace shi daga gidansa kusan shekaru bakwai da suka gabata.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi na neman INEC ta sauya jadawalin zaben 2027 domin Musulmai

A jiya Juma’a sufeto-janar na ‘yan sanda, Olatunji Rilwan Disu, ya umarci sashen kula da korafe-korafe na rundunar da ya binciki takardar koke da ke alakanta wasu manyan jami’an ‘yan sanda da zargin kashe Dadiyata.

Takardar koken ta fito ne daga wani lauya dan Kano mai suna Abba A. Hikima, wanda ya bukaci a binciki zargin da wani tsohon hadimin Bello Matawalle mai suna Muhammad Musa Kamarawa ya yi.

Ganduje ya yi martani ga Dadiyata

Mun ba ku labarin cewa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya tanka wa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai kan batun bacewar Abubakar Idris, watau Dadiyata a 2019.

Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa ya bayyana zargin da Malam El-Rufai ya jingina masa a matsayin mara tushe ballantana makama.

Ganduje ya nuna tausayawa ga iyalan Abubakar Idris 'Dadiyata', yana mai cewa abin da ya kamata a mayar da hankali a kai shi ne gano gaskiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.