Kano: Barkewar amai da gudawa ta janyo rasa rayuka 15, 40 suna asibiti kwance

Kano: Barkewar amai da gudawa ta janyo rasa rayuka 15, 40 suna asibiti kwance

- Mazauna kauyen Koya dake karamar hukumar Minjibir ta jihar Kano sun fada juyayi bayan mutum 15 sun rasu

- Wata cuta ce ta barke wacce ake zargin kwalara ce sakamakon amai da gudawa da mutanen suke ta yi

- Tuni jami'an lafiya suka bukaci mazauna kauyen da su kauracewa ruwan tafkuna da rijiyoyinsu

A kalla mutum 15 ne suka rasa rayukansu a kauyen Koya dake karamar hukumar Minjibir ta jihar Kano bayan zargin barkewar cutar amai da gudawa a yankin.

Dagacin kauyen, Sulaiman Muhammad, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai inda yace annobar ta fi shafar mata da kananan yara.

Mazauna kauyen da suka zanta da manema labarai sun ce wadanda cutar ta shafa suna ta kwarara amai da gudawa.

KU KARANTA: Batancin ga Annabi: Duk da shigar 'yan sanda, ana cigaba da rikici a Legas

Kano: Barkewar amai da gudawa ta janyo rasa rayuka 14, 40 suna asibiti kwance
Kano: Barkewar amai da gudawa ta janyo rasa rayuka 14, 40 suna asibiti kwance. Hoto daga @TheCableng
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan ta'addan ISWAP sun tarwatsa sansanin soji a jihar Borno

Jami'an lafiya da suka isa kauyen bayan aukuwar lamarin sun hori mazauna kauyen da su guji shan ruwa daga tafkuna da rijiyoyin kauyen.

An tattaro cewa jami'ai sun kai jakkuna ruwan leda 300 kauyen a ranakun karshen mako domin takaita cigaban yaduwar muguwar annobar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Aminu Tsanyawa, bai dauka wayar da aka dinga kiransa ba domin jin martanin gwamnatin jihar a kan lamarin.

A wani labari na daban, Dino Melaye, tsohon sanatan da ya taba wakiltar Kogi ta yamma, yace shugaban kasa Muhammadu koyaushe baya nan kuma bashi da lokaci.

Jigon jam'iyyar PDP yace ba zai yuwu shugaban kasan ya ki yi wa kowa magana ba sai ta bakin masu magana da yawunsa, TheCable ta wallafa.

Ya ce shirun Buhari na da matukar illa ga yaki da rashin tsaro a kasar nan. Melaye ya sanar da hakan ne a yayin tattaunawar da aka yi da shi a AIT ranar Juma'a.

"Akwai bukatar shugaban kasa yayi magana kai tsaye da 'yan Najeriya, akwai bukatar yayi magana da kafafen yada labarai. Tamkar babu shugaban kasa kuma hakan yana da matukar illa ga yaki da ta'addanci a kasar nan," yace.

"Abun takaici ne. Babu abinda muke ji illa fadar shugaban kasa tace kaza da kaza. Ba mu zabi Garba Shehu da Adesina ba."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng