Latest
Kenneth Okonkwo, kakakin kwamitin kamfen Atiku Abubakar, ya ce duk wanda ke goyon bayan ci gaba da sayar da fetur kan N1,300 bai cancanci jagorantar Najeriya ba.
Igho Ubiribo, ɗan kasuwa ɗan Najeriya a Birtaniya, ya rasu bayan allurar ƙara girman mazakuta karo na biyar, yayin da Thailand ke binciken asibitin.
'Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro na 'yan sa-kai na KADVS uku a Kubau, Kaduna, yayin da aka kuma sace ƙanin ɗan majalisar dokokin jihar a wani hari daban.
Sarkin Aresaadu na Iresaadu a jihar Oyo ya roƙi gwamnatin Oyo ta dakatar da shirin nada wani sarki na daban, yana mai cewa hakan ya saba wa umarnin kotu.
Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta nuna damuwa kan yadda ake gudanar da shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i.
Yan bindiga sun kai hare-hare a wasu kauyuka da ke kananan hukumomin Giwa da Kubau na jihar Kaduna, inda suka kashe mutane biyar tare da yin garkuwa da wasu 27.
Nasir Yusuf Gawuna ya ƙi komawa APC duk da komawar manyan mutanen sa na siyasa, yayin da aka ce ya ci gaba da zama a NDC domin zaɓen Kano na 2027.
Rundunar yan sandan Adamawa sun gurfanar da Dahiru Garba mai shekaru 87 bisa zargin sare hannun alkalin kotun Fufore da adda yayin zaman shari’a.
Lauyar Khadija Diab ta ce matar 'yar kasar Moroccan ɗin ta koma ƙasarta tun Afrilu 2026 kuma tana zaune tare da iyalanta, ba tare da Sheikh Ahmad Gumi ba.
Masu zafi
Samu kari