Ta Faru Ta Kare: An Yanke wa Mutum 3 Hukuncin Daurin Rai da Rai kan Sace Daliban Oyo

Ta Faru Ta Kare: An Yanke wa Mutum 3 Hukuncin Daurin Rai da Rai kan Sace Daliban Oyo

  • Kotu ta yanke wa mutum uku daurin rai da rai bayan sun amsa laifin hannu a garkuwa da dalibai da malamai a jihar Oyo
  • Wadanda aka daure sun amsa kasancewa mambobin haramtacciyar kungiyar ta'addanci tare da boye bayanan ayyukan kungiyar ga hukumomi
  • Kotu ta umarci a fara kirga wa'adin hukuncin daga ranar da jami'an tsaro suka kama su domin gurfanar da su gaban shari'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa wasu mutum uku hukuncin daurin rai da rai saboda hannu a sace dalibai da malamai a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo.

Kotun ta bayyana cewa za a fara kirga wa'adin hukuncin Abdulrazak Umar, wanda aka fi sani da Abu Khalifa ko Abu Khalid; Yunusa Musa, wanda ake kira Yunusa Bin Musa; da kuma Shamsu Adamu Sani, wanda aka fi sani da Abu Itisar, daga ranar da jami'an tsaro suka kama su.

Kara karanta wannan

ICPC ta gano ma'aikatan bogi 908, 'yan sanda ne kan gaba

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wa mutum 3 hukuncin daurin rai da rai kan harin Oyo.
Harabar babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Masu laifin sun roki kotu

Kafin Mai Shari'a Salim Ibrahim ya yanke hukuncin, lauyan wadanda ake tuhuma ya roki kotu da ta yi musu sassauci wajen yanke hukunci, in ji rahoton Channels TV.

Ya bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da suka aikata laifi kuma sun amsa laifukan da ake tuhumarsu da su ba tare da bata lokaci ba.

Lauyan ya ce hakan ya nuna sun yi nadama kan abin da suka aikata, yana mai cewa ba dukkan tuhume-tuhumen da aka yi musu ba ne suka shafi garkuwa da mutane.

Ya kara da cewa dukkansu maza ne masu iyali, suna da yara da kuma iyaye tsofaffi da ke dogaro da su, don haka ya roki kotu da ta ba su wata dama ta biyu ta rayuwa ta hanyar rage musu hukunci.

Sai dai lauyan masu gabatar da kara ya shaida wa kotu cewa wadanda ake tuhuma sun san masu aikata ta'addanci da ke cikin daji, amma maimakon su sanar da hukumomin tsaro, suka boye bayanan.

Kara karanta wannan

Yadda dan takarar gwamna ya kawo ƙarshen rikicin shugabancin ADC a Kaduna

Sun amsa laifin ta'addanci

Punch ta rahoto cewa, bayan an karanta musu tuhume-tuhumen, mutum ukun sun amsa cewa su mambobin haramtacciyar kungiyar ta'addanci ne.

A lokacin da aka gurfanar da su a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin aikata ta'addanci, sun kuma amsa laifin boye bayanai game da shiryawa da aiwatar da sace dalibai da malamai.

Sai dai mutum na farko, Abdulrazak Umar, shi kadai ne ya amsa laifuffuka da ke cikin tuhume-tuhume na bakwai zuwa na goma, wadanda suka shafi ba da horo, isar da umarni da kuma tunzura mambobin kungiyar ta'addanci kan wata akida ta addini.

Kotu ta ce wadanda suka gabatar da kara sun kawo kwararan hujjoji da suka tabbatar da laifin wadanda ake kara
Fuskokin mutane 3 da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai kan garkuwa da dalibai da malaman makarantar Oyo. Hoto: UGC
Source: UGC

Yadda DSS ta gurfanar da su

Hukumar Tsaro ta DSS ce ta gurfanar da mutum ukun a gaban kotu kan tuhume-tuhume guda 10 da suka hada da garkuwa da mutane, boye bayanai da kuma aikata laifukan da suka shafi ta'addanci.

Bisa ga takardun karar, dukkansu 'yan asalin jihar Neja ne, kuma ana zarginsu da boye bayanai game da mutanen da ke da alaka da ayyukan ta'addanci, shiga harkar garkuwa da mutane, da kuma amfani da wani dandali na sadarwa wajen gudanar da horo ga mambobin kungiyar ta'addanci.

Kara karanta wannan

Matukan tankar mai sun ruga da gudu a Hormuz yayin da Iran ke barin wuta

Majalisa ta tallafawa iyalan makarantar Oyo

A wani labari, mun ruwaito cewa, najalisar Dattawan Najeriya ta bada tallafin Naira miliyan 50 ga iyalan mutum biyar da suka mutu a ƙokacin ceto daliban Oyo.

Rahoto ya nuna cewa malamai biyu sun mutu a hannun masu garkuwa, yayin da jami’an tsaro uku suka rasu a aikin ceton.

Dakarun sojoji da wasu jami'an tsaro sun yi nasarar kubutar da dalibai 39 da malamai bakwai bayan sace su a jihar Oyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com