Ana Sayar da Kiristocin Arewa a matsayin Bayi a Najeriya? An Ji Gaskiyar Zance
- An yi ta yada wasu rahotanni da ke nuni da cewa ana sayar da Kiristocin Arewacin Najeriya a matsayin baya
- Binciken hotuna da bidiyon ya nuna an ɗauke shi ne a wata kasa ne cikin Mayun 2026, inda jami'an tsaro suka kama wasu fararen hula
- Rahoton ya bayyana cewa babu wata hujja da ke nuna lamarin ya faru a Najeriya, don haka ikirarin da aka yaɗa ƙarya ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wasu rahotanni sun yi ta yawo a kafofin sadarwa a Najeriya inda aka wai ana sayar da Kiristoci a matsayin bayi a Arewacin Najeriya.
Wannan saƙo ya bazu sosai a shafukan sadarwa da ake da su lamarin da ya jawo cece-kuce tsakanin masu amfani da kafafen sada zumunta.

Source: Getty Images
Rade-radi kan mayar da Kiristocin Arewa baya

Kara karanta wannan
Ministan Tsaro: Abin da ya hana sojoji gwabza wa da ƴan bindiga don ceto ɗaliban Oyo
Wani mai amfani da Instagram mai suna @Apostleamosngosha ya wallafa wani bidiyo yana ikirarin cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya tare da ɗaure wasu ana sayar da su bayi.
A cikin bidiyon an ga maza da mata suna tafiya a jere da hannayensu a ɗaure a baya, yayin da wasu dauke da makamai sanye da kayan jami'an tsaro ke rakiyarsu.
Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun amince da ikirarin, yayin da wasu suka nuna shakku kan sahihancinsa.
Binciken gaskiya kan rade-radin a Najeriya
Saboda muhimmancin batun, Dubawa ta gudanar da bincike domin tantance gaskiyar ikirarin.
Da farko ta yi binciken kalmomi masu alaƙa da lamarin, amma ba ta samu wata hujja daga Najeriya da ke tabbatar da wannan batu ba.
Masu binciken sun yi amfani da fasahar binciken hotuna da bidiyo, inda suka gano cewa an fara wallafa wannan bidiyo tun a watan Mayun 2026, watanni kafin a danganta shi da Najeriya.

Source: Facebook
Binciken ya kai zuwa wani shafin labarai na Kivumorningpost.cd, wanda ya wallafa bidiyon yana cewa ya nuna fararen hula daga Kivu ta Kudu da aka kama a yankin Kunda da ke lardin Ituri a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

Kara karanta wannan
Da gaske Tinubu, ministocinsa sun manta sun rera tsohon taken Najeriya? Gaskiya ta fito
Daga nan kuma an gano wani rahoton da ya bayyana cewa jami'an tsaro sun kama mutanen ne saboda sun yi zargin shigowarsu yankin cikin yanayi mai tayar da hankali.
Sai dai majiyoyin yankin sun ce yawancin mutanen matasa ne daga Kivu ta Kudu da suka isa Kunda domin aikin noma da kuma hakar zinari, rahoton bai ambaci Najeriya ko Kiristocin Najeriya ba.
A karshe dai, lamarin ya faru ne a Kongo, ba a Najeriya ba, kuma babu wata hujja da ke nuna ana sayar da Kiristocin Arewacin Najeriya bayi kamar yadda aka yi ikirari.
Kiristoci sun fusata kan kisan malamar Islamiyya
Mun ba ku labarin cewa shugabannin Kiristoci a Arewacin Najeriya sun yi alhini da ta'aziyya ga iyalan Malama Ummulkhairi Usman Aliyu.
Kiristocin sun kuma yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa malamar Islamiyan a Maraban Jos, jihar Kaduna.
Sun buƙaci gwamnati ta kamo tare da hukunta duk masu hannu a wannan mummunan kisa da aka yi wa malamar.
Asali: Legit.ng