Rikicin da Aka Samu a Majalisa da Aka Amince da Kudurin Kafa 'Yan Sandan Jihohi
- Majalisar Wakilai ta amince da kudirin kafa 'yan sandan jihohi bayan kuri'ar da 'yan majalisa 311 suka kada a kan hakan
- Rahoto ya nuna cewa wasu 'yan tsiraru daga cikin 'yan majalisar sun fice daga zauren majalisa, sun yi zargin cewa an karya tsarin doka
- Shugaban majalisa ya ce 'yan majalisa 35 sun kada kuri'a ta yanar gizo, 276 kuma sun kada kuri'arsu a zauren majalisar a ranar Alhamis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Abuja - Majalisar Wakilai ta amince da kudirin gwamnatin tarayya na kafa rundunar 'yan sandan jihohi bayan kuri'ar da 'yan majalisa 311 suka kada domin goyon bayan gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya.
Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya bayyana cewa 'yan majalisa 35 ne suka kada kuri'arsu ta yanar gizo, yayin da wasu 276 suka kada kuri'a a cikin zauren majalisa.

Source: Facebook
Kudirin ya tanadi kafa 'yan sandan jihohi
An cimma wannan matsaya ne bayan da majalisar ta tattauna tare da amincewa da rahoton Kwamitin Bita kan Kundin Tsarin Mulkin 1999, wanda Mataimakin Shugaban Majalisa, Benjamin Kalu, ke jagoranta, in ji rahoton Vanguard.
Rahoto ya nuna cewa kudirin na neman yin gyaran kundin tsarin mulki domin samar da tubalin doka da zai bai wa jihohi damar kafa rundunonin 'yan sanda.
Rahotanni sun nuna cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ne ya mika kudirin ga Majalisar Wakilai domin a yi masa nazari.
'Yan tsiraru sun kaurace wa zama
Sai dai bayan amincewar da aka yi da kudirin, 'yan tsiraru a majalisar sun fice daga zauren domin nuna rashin amincewarsu da yadda aka gudanar da zaman.
Da yake magana da manema labarai bayan ficewar, Jagoran 'Yan Tsiraru, Fredrick Agbedi, ya ce ba sa adawa da kafa 'yan sandan jihohi, amma suna adawa da yadda shugabancin majalisar ya gudanar da tsarin amincewa da kudirin.
A cewarsa, an yi watsi da tanade-tanaden kundin tsarin mulki da kuma dokokin majalisar yayin tattaunawa kan kudirin.
'Yan majalisar sun yi zargin an karya doka
Jaridar Punch ta rahoto Agbedi ya bayyana cewa kundin tsarin mulki shi ne tushen dukkan dokoki, saboda haka bai kamata shugaban majalisar ya yi watsi da tanade-tanaden Sashe na 9(2) na kundin tsarin mulki ba.

Source: Twitter
Ya kuma ce halartar 'yan majalisa ya kamata ta kasance bisa rajistar halarta da ake sanyawa hannu a kowace rana, ba wai ta hanyar kirga sunayen da aka karanta a zauren ba.
'Yan tsirarun sun kara da cewa dokokin majalisar sun tanadi cewa dole ne a tattauna kudirin gyaran kundin tsarin mulki sashe bayan sashe, kuma kowanne sashe ya samu goyon bayan akalla kashi biyu bisa uku na 'yan majalisar.
Sun yi zargin cewa shugaban zaman ya karanta taken kudirin kawai, sannan aka yi amfani da kuri'ar murya wajen amincewa da shi ba tare da yin cikakken nazarin sashe-sashe kamar yadda doka ta tanada ba.
Asali: Legit.ng

