Jarumar Fim na Kwance a Asibiti, Ta Roki Jama'a Tana Maganar Mutuwa

Jarumar Fim na Kwance a Asibiti, Ta Roki Jama'a Tana Maganar Mutuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

  • Fitacciyar jarumar Nollywood, Ngozi Nwosu, ta bayyana cewa ta kwashe makonni uku tana jinya a asibiti saboda rashin lafiya
  • Jarumar ta ce likitoci sun shirya yi mata tiyata har sau uku, lamarin da ya sa ta roƙi magoya bayanta su taimaka mata da kuɗi
  • Bidiyon da ta wallafa daga gadon asibiti ya tayar da hankalin masoyanta da abokan aikinta, inda suka yi mata addu'o'in samun lafiya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas – Fitacciyar jarumar masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood, Ngozi Nwosu, ta roƙi magoya bayanta da masoyanta su taimaka mata da kuɗi bayan ta kwashe makonni uku tana jinya a asibiti.

Ngozi Nwosu ta ce rashin lafiyarta ya kai matakin da ba za ta iya ɗaukar nauyinta ita kaɗai ba, saboda haka tana buƙatar taimakon jama'a.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali: Wani uba da ƴarsa sun rasu bayan sun fada rijiya a Kano

Jaruma Ngozi Nwosu
Jarumar fim Ngozi Nwosu da ke neman agaji. Hoto: @ngozinwosu
Source: Instagram

Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo mai cike da tausayawa da ta wallafa a shafinta na Instagram a ranar 23 ga Yulin 2026, inda aka ganta tana kwance a gadon asibiti cikin yanayi na rashin lafiya.

Halin da jaruma Ngozi ke ciki

A cikin bidiyon, jarumar ta ce ta shafe makonni uku tana kwance a asibiti, kuma likitoci sun shirya yi mata tiyata har sau uku.

Ta ce:

"Mutanena, masoyana da iyalaina, na san kun daɗe ba ku gan ni ba. Na kwashe makonni uku ina kwance a asibiti. Don Allah, lamarin ya fi ƙarfina. Ina buƙatar taimakonku. Kada ku bar ni na mutu."

Jarumar ta bayyana cewa tana cikin matsanancin ciwo, tana mai cewa tana fatan Allah zai ba ta lafiya, amma tana roƙon masoyanta kada su yi watsi da ita a wannan mawuyacin lokaci.

Wadanda za a tuntuba

Ngozi Nwosu ta ce duk wanda yake son taimaka mata zai iya tuntuɓar tawagar da ke kula da harkokinta domin samun cikakken bayani kan yadda za a ba da gudummawa.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An gano jami'ar bogi da ta tara dalibai a Najeriya

Ta kammala saƙonta da addu'a, inda ta ce:

"Ina roƙon Allah kada ya sa wani ya shiga irin wannan rashin lafiya da nake ciki. Na gode."
Jarumar Nollywood, Ngozi Nwosu
Ngozi Nwosu kafin rashin lafiya ya kamata. Hoto: @ngozinwosu
Source: Instagram

Masoya sun yi mata addu'a

Bayan bidiyon ya bazu a kafafen sada zumunta, magoya bayanta da abokan aikinta a masana'antar Nollywood sun cika sashen sharhi da saƙonnin addu'a da fatan Allah ya ba ta lafiya cikin gaggawa.

Mutane da dama sun bayyana alhininsu kan halin da jarumar ke ciki, tare da yi mata fatan samun waraka da kuma samun taimakon da take buƙata.

Ga bidiyon da ta yi bayani:

Jarumar fim ta caccaki Rarara

A wani labarin, mun kawo muku cewa jarumar Kannywood, Mansurah Isah ta caccaki mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara.

Jarumar ta bayyana cewa tunda ta fita daga tafiyar Rarara ta Triple R ba ta yi magana amma lokaci ya yi da za ta daina shiru kan abubuwan da suka faru.

Maganar Mansurah na zuwa ne bayan bullar barazana a tafiyar Rarara bisa zargin wasu makudan kudi da aka ba su a Gombe da kuma wajen Abdulaziz Yari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng