Baki Abin Magana: Ndume Ya Yi Fade Fade bayan Ganawa da Tinubu
- Sanata Ali Ndume ya bukaci shugaba Tinubu da ya daina tura hadimansa su yi jawabi a madadin sa, ya fito kai tsaye ya yi magana da jama'a
- Ndume da ya ziyarci Aso Rock ya tattauna da Tinubu kan rashin tsaro, tsadar kayayyaki da halin da jama'ar Arewa maso gabas ke ciki
- Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin duba korafin, haka kuma ya nemi a rika gudanar da irin wannan tattaunawa da Sanata Ndume akai-akai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ya yi korafi da cewa shugaba Bola Tinubu ya dogara sosai kan masu magana da yawunsa, alhali al'umma na jiran ji kalamansa kai tsaye.
Ndume ya bayyana haka ne bayan ya gana da shugaban kasa a fadar Aso Rock ranar Alhamis, inda ya nuna damuwarsa game da kasancewar shugaban kasa ya yi nesa da jama'a.

Source: Facebook
Abin da Ndume ya fadawa Tinubu
Punch ta rahoto cewa Sanata Ndume ya ce shugaban kasa ya dauki lokaci mai tsawo ba tare da ya yi wa jama'a bayani kai tsaye ba.
Ya ce:
"Na gaya wa shugaban cewa ya rika magana da jama'a. Na ba shi shawara kuma ya yi alkawarin zai duba kan hakan ya kuma yi magana kai tsaye da 'yan Najeriya.
"Mutane suna jiran shugabansu ya gaya musu yadda abubuwa ke tafiya, ba wai ya tura wasu su yi magana a madadin sa ba. Ya dauki lokaci mai tsawo bai yi magana kai tsaye da 'yan Najeriya ba, kuma wannan ya na da matukar muhimmanci,"
Sanatan ya bayyana cewa ganawar ita ce karo na farko da ya hadu da shugaban bayan dogon lokaci, inda tattaunawar ta shafi batutuwa irin su rashin tsaro, tsadar rayuwa da sauransu.
Martanin Tinubu ga Ndume
Ndume ya shaida cewa shugaban kasar ya nuna matukar farin ciki da tattaunawar, har ya nemi a rika gudanar da irin wannan ganawa akai-akai.
"Shugaban ya ma dage cewa ya kamata mu rika yin haka, ba lalle ne a ofis inda mutane ke shiga su fita a kowane lokaci ba, a wani wuri, mai yiwuwa a gidansa, domin mu rika magana tare kan yadda za a warware wasu daga cikin waɗannan matsaloli,"
In ji Ndume.
The Cable ta wallafa cewa ya kara da cewa ya yi irin wannan ganawa a baya amma ta tsaya, sai kuma yanzu ta sake dawowa, kuma shugaban ya nuna yana son hakan.

Source: Facebook
Tsokaci kan tsaro da tattali
Kan batun rashin tsaro, Ndume ya ce an rage tashin hankali a yankin Arewa maso Gabas, domin yanzu hankali ya fi karkata zuwa Kudu, Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma.
Ya lura cewa kafin ganawar, ya jira Tinubu domin shugaban yana zama da shugabannin sojoji a wani taron tsaro, wanda ya ɗauka a matsayin hujja ta cewa Tinubu yana aiki tukuru.
Kan tattalin arziki, sanatan ya ce tsadar mai, abinci da sufuri na ci gaba da damun jama'a, amma ya bayyana yakinin sa cewa gwamnati za ta iya daukar matakin da ya dace.
Kiran Tinubu ga 'yan Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan halin da ake ciki na tsadar rayuwa a Najeriya.
A bayanin da ya yi, Bola Tinubu ya bukaci dukkan 'yan kasa su kwantar da hankalinsu, domin a cewar shi, da sannu kowa zai sharbi romon dimokuradiyya.
Shugaban kasar ya yi magana ne yayin da 'yan Najeriya da dama ke korafi game da yadda salon mulkinsa ke tafiya a lokacin da ya ke neman tazarce.
Asali: Legit.ng


