Rikicin ADC Ya Sauya Salo a Jihar Kano, Lamari Ya Kai ga Yan Sanda
- Rikicin shugabanci a ADC reshen jihar Kano ya kara tsananta bayan tsagin Musa Shu'aibu ya yi kakkausan martani ga jagora a jam'iyyar, Naja'atu Bala Muhammad
- Bangaren da Hon. Musa Shu'aibu Ungogo ke jagoranta ya zargi Hajiya Najaatu Muhammad da kafa kwamitin riƙon ƙwarya ba bisa kundin tsarin mulkin jam'iyyar ba
- Tsagin ya bayyana cewa ba zai zauna ya lamunci matakin da Naja'atu ta zo da shi ba, inda ya dauki mataki zuwa rundunar yan sandan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam'iyyar ADC a jihar Kano ya ɗauki sabon salo, bayan al'amari ya kai gaban 'yan sanda.
Wani bangare na jam'iyyar ya shigar da ƙara gaban rundunar 'yan sandan jihar kan abin da ya kira yunkurin tada rikici a cikin jam'iyyar.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta kawo labarin cewa kwamitin riƙon mulki na ADC na jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Hon. Musa Shu'aibu Ungogo ya aika takardar ƙorafi mai kwanan wata 8 ga Yulin 2026 ga kwamishinan 'yan sandan jihar.
Rikici ya dabaibaye ADC a Kano
A cikin takardar, bangaren ya zargi Hajiya Najaatu Muhammad da ƙoƙarin raba kan jam'iyyar ta hanyar kafa kwamitin riƙon ƙwarya na reshen Kano ba tare da bin tanadin kundin tsarin mulkin jam'iyyar ba.
Sun bukaci rundunar 'yan sanda ta shiga tsakani tare da gudanar da bincike kan abin da suka bayyana a matsayin haramtattun matakai da ka iya janyo matsalar tsaro da zaman lafiya a jihar.
Wannan ya biyo bayan sanarwar da Najaatu ta yi a farkon makon nan, inda ta bayyana kanta a matsayin mataimakiyar shugaban ADC ta ƙasa mai kula da yankin Arewa maso Yamma.
Haka kuma ta sanar da rusa kwamitin zartarwa na jam'iyyar a Kano da kuma naɗa kwamitin riƙon ƙwarya ƙarƙashin jagorancin Alhaji Umar Bala.
ADC ta caccaki Naja'atu
Sai dai bangaren shugabancin ADC na Kano ya yi watsi da matakin, yana mai cewa ya saɓa wa kundin tsarin mulkin jam'iyyar kuma bai samu amincewar hukumomin da suka dace ba.

Source: Original
Takardar ƙorafin da Hon. Ungogo da sakataren gudanarwa na jam'iyyar, Dr. Bala M. I. Takai, suka sanya wa hannu ta ce Najaatu ta yi hakan ne domin haddasa ruɗani da kuma raunana tsarin shugabancin jam'iyyar da ake da shi.
Sun ce ikon kafa kwamitin riƙon ƙwarya na jam'iyya yana hannun Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) ko Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC), ba ikon mutum ɗaya ba ne.
A cewarsu:
"Ikon kafa kwamitin riƙon ƙwarya yana hannun Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) ko Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC) ta hanyar umarni da ya dace. Babu wani jami'in jam'iyya guda da ke da wannan iko."
ADC ta yi magana kan tsare El-Rufa'i
A baya, kun samu labarin cewa jam'iyyar adawa ta ADC ta zargi gwamnatin APC da Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta da kokarin tsare tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, har sai bayan zaben 2027.

Kara karanta wannan
Tambuwal ya fadi dalilin 'yan siyasa na shiga ADC bayan karbar ciyaman da ya yi murabus
Mai magana da yawun jam'iyyar na kasa, Bolaji Abdullahi da ya bayyana zargin ya ce jam'iyyar na ganin ana kakaba sharudan beli masu wahalar cikawa domin a ci gaba da tsare El-Rufai a hannun hukumomin kasar.
Bolaji Abdullahi ya kuma yi ikirarin cewa dole ne a kiyaye lafiyar tsohon gwamnan jihar Kaduna, domin idan wani abu ya faru da El-Rufai a tsare, shugaba Bola Tinubu ne zai dauki alhakin hakan.
Asali: Legit.ng

