PVC: Jihar Sokoto Ta Ayyana Ranar Hutu saboda Zaben 2027
- Gwamnatin Ahmed Aliyu ta jihar Sokoto ta bayar da hutu ga jama'ar ta domin ba su dama su karbi katin zabensu gabanin kada kuri'a a 2027 mai zuwa
- An ɗauki matakin ne domin bai wa waɗanda ba su yi rajistar zaɓe ba damar samun katin PVC da zai ba su damar kada kuria'a don zabaen wanda su ke so
- Gwamna Ahmed Aliyu ya bukaci duknin 'yan jihar da su ka kai shekarun yin rajista da su tabbatar da cewa sun kammala kafin ranar 26 ga Yulin 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto – Gwamnatin Ahmed Aliyu a Sokoto ta ayyana ranar Juma'a, 24 ga Yulin 2026, a matsayin ranar hutu ga ma'aikatan gwamnati a fadin jihar.
A bayar da hutun ne domin bai wa waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri'a amma har yanzu ba su yi rajistar zaɓe ba damar shiga aikin rajistar da hukumar INEC ke gudanarwa.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa sanarwar ta fito ne cikin wata takarda da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a na Gidan Gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, ya fitar a ranar Alhamis, 23 Yuli, 2026.
An bayar da hutu a Sokoto
Nigerian Tribune ta kawo labarin cewa Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin bai wa ma'aikatan gwamnati isasshen lokaci su yi rajista tare da kabar PVC kafin babban zaɓen shekarar 2027.
A cewarsa:
"Mun ayyana ranar Juma'a, 24 ga Yulin 2026 a matsayin ranar hutu domin bai wa ma'aikatan gwamnati da suka kai shekarun kaɗa ƙuri'a amma ba su yi rajista ba damar shiga aikin rajistar masu zaɓe tare da samun Katin Zaɓe na Dindindin."
Rokon gwamnan Sokoto ga jama'arsa
Ahmed Aliyu ya yi kira ga duk ma'aikatan gwamnati da suka cancanci yin zaɓe amma ba su yi rajista ba su yi amfani da wannan damar, yana mai jaddada cewa katin PVC ne kaɗai ke bai wa ɗan ƙasa damar amfani da haƙƙinsa na kaɗa ƙuri'a.

Source: Facebook
Ya ce:
"Ina kira ga duk ma'aikatan gwamnati masu cancanta su yi amfani da wannan ranar hutu su yi rajista kuma su karɓi katin PVC domin su samu damar shiga babban zaɓe mai zuwa."
Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa na ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da cewa ma'aikatan gwamnati ba su rasa damar sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora musu na shiga harkokin dimokuraɗiyya.
An dauki ma'aikatan tsaro a Sokoto
A baya, kun samu labarin cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu Sokoto, ya yaye rukuni na biyu na jami'an Sokoto Marshals guda 1,550 da aka ɗauko daga dukkan ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Gwamnan ya ce shirin ba wai samar da aikin yi kawai ba ne, har ila yau wata muhimmiyar dabara ce ta ƙarfafa tsaron al'umma, kare rayuka da dukiyoyi a Sokoto da ake fama da matsalar tsaro.
Gwamna Biodun Oyebanji na Ekiti ya yaba da matakin gwamnatin Sokoto, yana mai cewa wani abin koyi ne da sauran jihohin Najeriya za su iya kwaikwaya domin karfafa tsaro da kare rayukan jama'a.
Asali: Legit.ng

