Sheikh Guruntum Ya ba da Mamaki, Ya Gargadi Masu Masa Kirari

Sheikh Guruntum Ya ba da Mamaki, Ya Gargadi Masu Masa Kirari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

  • Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya yi gargadi ga mabiyansa kan masa kirari a lokacin wa'azi
  • Sheikh Guruntum ya bayyana cewa ba ya jin dadin yabon da ake masa saboda shi ma yana neman inganta imanin sa ne
  • Mutane daban daban sun yi tsokaci game da gargadin da malamin ya yi, inda wasu ke ganin ya cancanci a cigaba da masa kirari

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jiha Bauchi - Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum, wanda ake masa laƙabi da likitan zuciya, ya fito ya yi gargadi ga jama'a kan al'adar yabawa masana addini fiye da kima.

Wani bidiyo da ya bazu a kafofin sada zumunta ya nuna cewa Sheikh Ahmad Guruntum ya yi gargadin ne a wajen wa'azi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi wa sojoji ƙarin lbashi mai gwaɓi don inganta walwalarsu a Najeriya

Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf
Sheikh Ahmad Guruntum yana wa'azi a masallacin Annur da ke Abuja. Hoto: Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum
Source: Facebook

Gargadin da Guruntum ya yi

A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Ahmad Guruntum ya nuna cewa ba ya bukatar yawan kirari da al'umma ke masa.

Ya bayyane cewa mutane da dama suna yin gaggawar yaba masa da kirari kamar su "likitan zuciya" da sauran kalaman girmamawa, amma shi da kansa bai gamsu da irin wannan hali ba.

Ya nuna cewa shi ma kamar kowa ne, har yanzu yana yin fafutukar zama cikin bayin Allah nagari ne, kuma bai cancanci a ɗaukaka shi sama da matsayinsa na yau da kullum ba.

Guruntum ya ce:

"Wallahi ba haka ba ne, wallahi tallahi wannan maganar bana son ta, kuma idan ana fada bana jin dadi.
"Ba daidai ba ne. Ba na so."
"Don ni ma ina fama tawa zuciyar. Allah ya shiryar da mu."

Martanin jama'a ga Guruntum

Mutane da dama sun yi martani ga gargadin da malamin ya yi, inda Mansur Abubakar Zaidi ya ce:

Kara karanta wannan

Ibrahim Aliyu Kaduna ya bukaci a ba shi kwangilar magance daba a Kano

"Wato akwai tawali’u ga Malam."

Ismail T Jalo ya ce:

"Malam, ba ka fahimce mu ba ne! Saƙonka ake nufi, ba kai ba."

Fuad Ali Ridwan ya ce:

"Allah ya ƙara maka lafiya, Malam.:"

Adam Isah Adam cewa ya yi;

"Kaji manya fa, ita kanta wannan maganar mai gyara zuciya ce. Malam ka yi haƙuri, abin da ake nufi shi ne maganarka tana gyara zuciya, wallahi, tunda ayoyi ne da hadisai da maganganun magabata."

Alhaji Ali Adamu ya ce:

"Wallahi ba za mu daina ba har abada. Kawai ka yi haƙuri."

Zak S Clothing Brand ya ce:

"Likitan zuciyoyinmu. Tabbas Allah ya shiryar da mu ne ta sanadinka. Ka cancanci ka zama likitan zuciyar duk wani Musulmi mai neman shiriya. Yadda kake isar da saƙon Allah da na Manzon Allah (SAW) ne ya kai ka wannan matsayi. Wannan maganarka ta ƙara nuna tawali’u da ƙasƙantar da kai. Ina roƙon Allah Ya ƙara wa rayuwarka albarka, Ya azurta ka da kyakkyawan ƙarshe."

Kara karanta wannan

2027: Fadar shugaban kasa ta yi magana kan barazanar kashe Peter Obi

Alameen Malam ya ce:

"Za mu daina in sha Allah, amma wallahi wa’azinka ya fi na kowa ratsa min zuciya."

Sadiq Ajay Sani ya yi wa Sheikh Guruntum martani da cewa:

Sheikh Guruntum a Bauchi
Sheikh Ahmad Guruntum da masallacinsa a Bauchi. Hoto: Malam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum
Source: Facebook
"Allah Ya sani ina ƙaunar Malam saboda Allah. Kalmar 'Likitan Zuciya' mu masoya Malam a ganinmu yabonsa muke yi. Amma tunda Malam ya ce ba ya so, wallahi in sha Allah za mu daina faɗa masa. Za mu zama masu tarbiyya. Allah Ta’ala Ya sa mu dace."

Muhammad Haruna ya ce:

"In sha Allah daga yau na daina faɗa. Allah Ubangiji Ya shiga lamarinmu baki ɗaya."

Nasir Rabiu ya ce:

"Wannan tanbihi ya ƙara tabbatar min da cewa Malam likitan zuciya ne. Wato Malam na ƙoƙarin nuna wa mutane kada su riƙa son a riƙa yabonsu ko tsarkake su. Allah Ya karɓi aikin Malam."

A karshe, Malam K Garba ya ce:

"Sau da yawa mutane masu daraja a idon al'umma ba sa son ana kiransu masu daraja, gani suke kamar an kai su inda ba su kai ba, alhali sun ma wuce haka."

Kara karanta wannan

Da gaske alkalin da ya ba Tinubu nasara a kotu a zaben 2023 ya makance?

Sultan ya zauna da malamai

A wani labarin, mun kawo muku cewa mai alfarma Sarkin Musulmi ya zauna da malaman addinin Musulunci a Najeriya.

Shugaban Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau da sakatarensa, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe sun halarci zaman.

Wakilin Sheikh Sani Yahya Jingir, Dr Hassan Dikko da shugabannin Jama'atu Nasril Islam na cikin mahalarta taron da aka yi.

Haka zalika taron ya haɗa Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi da wasu manyan malamai a sassa daban-daban na Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng