Kasar Isra'ila Ta kai Hare Hare Gaza, Ta Kashe Falasdinawa
- Isra'ila ta kai sababbin hare-haren sama a yankunan Zirin Gaza bayan ta umarci mazauna wasu wurare su fice, lamarin da ya yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa biyu
- Rahotanni sun nuna cewa hare-haren sun afku ne duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani aka cimma a bara, yayin da rikicin ke ci gaba da tsananta
- Hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce sama da mutane miliyan 1.4 a Gaza na ci gaba da fuskantar matsananciyar yunwa da ƙarancin abinci duk da yarjejeniyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma ƙwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Gaza– Sojojin Isra'ila sun kai sababbin hare-haren sama a yankuna da dama na Zirin Gaza bayan sun fitar da umarnin ficewa ga mazauna wasu wurare, lamarin da ya yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa biyu.
Hare-haren sun afku ne a ranar Alhamis, inda suka lalata gidaje a sansanonin 'yan gudun hijira na Bureij da Jabalia da kuma unguwannin Zeitoun da Tal al-Hawa da ke birnin Gaza.

Source: Getty Images
Rahoto Al Jazeera ya ce jami'an tsaro da fararen hula sun ci gaba da kokarin kashe wata babbar gobara da ta tashi bayan wani harin da aka kai a birnin Gaza.
Isra'ila ta kai hare-hare Gaza
Dan jaridar Al Jazeera, Ibrahim al-Khalili, ya ce abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda hare-haren suka biyo bayan gargadin da aka yi wa mutane su bar yankunan da aka kai harin.
Ya bayyana cewa ga iyalan da ke Gaza, umarnin ficewa ba wai sauyin matsuguni kawai yake nufi ba, domin yana tilasta musu barin duk wata mafaka da suka samu cikin gaggawa.
Wani hari da aka kai wani gini a unguwar Zeitoun da ke kudu maso gabashin birnin Gaza ya kuma jikkata mutane da dama, kamar yadda majiyoyi daga asibitin al-Ahli suka tabbatar.
Rayuwa ta ta'azzara a Gaza
Rahoton Yahoo News ya nuna cewa, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta, halin jin kai a Gaza na ci gaba da tabarbarewa.

Kara karanta wannan
Ta faru ta kare: An yanke wa mutum 3 hukuncin daurin rai da rai kan sace daliban Oyo
A cewar hukumomin lafiya na Gaza, yaƙin ya yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 73,311, ciki har da sama da mutum 1,185 da aka kashe tun bayan tsagaita wutar da aka cimma a watan Oktoban 2025.
Haka kuma, wani sabon bincike da hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya suka gudanar ya nuna cewa kimanin mutane miliyan 1.4, wato kusan kashi 67% na al'ummar Gaza, har yanzu na fama da matsananciyar ƙarancin abinci.

Source: Getty Images
Daraktan shirye-shiryen gaggawa na Hukumar Abinci ta Duniya (WFP), Ross Smith, ya ce har yanzu halin da ake ciki a Gaza yana da matuƙar muni, yana mai kira da a ci gaba da bai wa ayyukan agaji cikakken goyon baya.
Masar ta yi magana kan Gaza
A gefe guda kuma, Ministan Harkokin Wajen Masar, Badr Abdelatty, ya bukaci Ministan Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, da a gaggauta tura Rundunar Tabbatar da Zaman Lafiya ta Ƙasa da Ƙasa (ISF) zuwa Gaza.
An bayyana cewa Masar na son a fara aikin kwamitin da zai kula da gudanar da harkokin Gaza domin rage tashin hankali da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.
Rahotanni daga kafafen yaɗa labaran Isra'ila sun kuma ce jami'an tsaro 30 daga Morocco sun kai ziyara Gaza a shirye-shiryen tura jami'ansu, yayin da Morocco ta sanar da shirin kafa asibitin filin yaƙi a yankin.
Batun yarjejeniya da Saudi
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugabannin jam'iyyun adawa a Isra'ila sun soki yarjejeniyar haɗin gwiwar nukiliya da Amurka ta kulla da Saudiyya.
Ma'aikatar Makamashi ta Amurka ta bayyana cewa Washington da Riyadh sun rattaba hannu kan yarjejeniyar amfani da fasahar nukiliya domin ayyukan farar hula.
Yarjejeniyar za ta bai wa Saudiyya damar bunƙasa shirinta na makamashin nukiliya cikin lumana, amma har yanzu tana jiran amincewar Majalisar Dokokin Amurka kafin ta fara aiki.
Asali: Legit.ng

