Baraka a APC, Tsohon Minista Ya Fadi Matsayarsa kan Amincewa da Zaben Fitar da Gwani
- Masu goyon bayan tsohon minista sun yi karin haske kan rahoton cewa magoya bayansa sun amince da sakamakon zaben fitar da gwanin APC a Bauchi
- Wasu da suka bayyana kansu a matsayin magoya bayan Yusuf Maitama Tuggar sun goyi bayan dan takarar APC
- Kungiyar Tuggar ta jaddada cewa ba a gudanar da sahihin zaben fitar da gwani na APC a Bauchi ba, tana mai cewa tana nan daram cikin jam'iyyar APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya yi martani kan rahoton cewa suna goyon bayan zaben fitar da gwani a Bauchi.
Tuggar ya musanta rahotannin da ke cewa magoya bayansa sun amince da sakamakon zaben fitar da gwani na gwamna na jam'iyyar APC a Bauchi.

Source: Facebook
Hakan na cikin sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Alkasim Abdulkadir, ya fitar, cewar Vanguard.
An ƙaryata rahoton goyon bayan Tuggar ga MA
Kungiyar yakin neman zabensa ta bayyana cewa rahoton ba gaskiya ba ne kuma ba ya wakiltar matsayinta.
kungiyar ta ce an yada bayanan da suka saba da matsayinta. Ta ce ba ta taba amincewa da sakamakon zaben fidda gwani ko sauya goyon bayanta ba.
Martanin ya biyo bayan taron manema labarai da wasu mutane da suka bayyana kansu a matsayin magoya bayan tsohon ministan harkokin wajen Najeriya suka gudanar a Bauchi.
A yayin taron, kungiyar karkashin jagorancin Musa Abdullahi ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar gwamna na APC, Mohammed Abdullahi Abubakar (SAN), gabanin babban zaben 2027.
Sai dai kungiyar Tuggar ta ce mutanen da suka yi wannan sanarwa sun amince da kansu cewa ba su wakiltar Ambasada Tuggar.

Source: Twitter
Matsayar Tuggar kan zaben fitar da gwani
Kungiyar ta kara da cewa abin da mutanen suka fada ra'ayinsu ne na kashin kansu, don haka bai kamata a dauke shi a matsayin matsayar Tuggar ko magoya bayansa ba.
Har ila yau, kungiyar ta sake jaddada cewa ba a gudanar da ingantaccen zaben fidda gwani na APC a Bauchi ba.
Ta ce tsarin da aka bi wajen fitar da dan takarar bai samu cikakkiyar tattaunawa da amincewar duk masu neman takara da manyan masu ruwa da tsaki ba.
A cewar sanarwar, saboda haka ba za a iya kallon tsarin a matsayin sahihin zaben maslaha da ya dace da ka'idojin dimokuradiyyar cikin gida ta jam'iyya ba.
Kungiyar ta ce Ambasada Tuggar yana nan daram cikin APC, yana mutunta kundin tsarin jam'iyyar da kuma bin doka da oda, cewar Punch.
Ta kuma bukaci kafafen yada labarai su rika bambance tsakanin ra'ayin wasu kungiyoyi masu zaman kansu da kuma matsayar hukuma ta Kungiyar Yakin Neman Zaben Tuggar.
A karshe, kungiyar ta ce magoya bayan Ambasada Tuggar suna cikin dukkan kananan hukumomi 20 na Bauchi, don haka ba za a iya cewa wasu tsirarun mutane ne ke wakiltarsu ba.
Masoyan Tuggar sun soki tikitin MA a Bauchi
An ji cewa magoya bayan tsohon Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar, sun yi korafi game da zaben fitar da gwanin gwamna a APC.
Gidauniyar Tuggar ta ce ba a gudanar da zaɓen fitar da gwani ba a Bauchi, saboda haka sanarwar ta saba doka.
Ta buƙaci shugabannin APC su sake duba lamarin, su tabbatar da adalci, dimokuraɗiyyar cikin gida.
Asali: Legit.ng


