Trump Ya Ware Kasar Afrika 1, Yana Shirin kai Farmakin Soji Cikinta

Trump Ya Ware Kasar Afrika 1, Yana Shirin kai Farmakin Soji Cikinta

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump na nazarin ƙaddamar da hare-haren soji kan wata ƙungiya mai alaƙa da al-Qaeda a ƙasar Mali
  • İdan har aka amince da harin, Mali za ta zama ƙasa ta takwas da Amurka za ta kai wa hari tun bayan dawowar Trump kan mulki karo na biyu
  • Gwamnatin tana nazarin kai harin ne kan ƙungiyar JNIM, wadda ta amsa alhakin ƙaddamar da hare-hare da sace-sacen mutane a Afirka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Gwamnatin Shugaba, Donald Trump, tana nazarin ƙaddamar da harin soji kan wata ƙungiya mai alaƙa da al-Qaeda a ƙasar Mali.

Irin wannan mataki na iya maida ƙasar Mali ta takwas da gwamnatin Trump za ta kai wa hari tun bayan dawowarsa kan karagar mulki a wa'adi na biyu.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun bani, Shugaba Tinubu ya fadada rundunar sojojin Najeriya

Shugaba Donald Trump
Donald Trump dauke da bindiga. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Independent ta wallafa cewa Amurka tana auna yuwuwar kai harin ne kan ƙungiyar Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), wadda ta amsa alhakin ƙaddamar da jerin hare-haren fitina da sace-sacen mutane tun bayan kafa ta a shekarar 2017.

Shirin kai harin Amurka

Ƙungiyar ta JNIM, wadda ke kawance da al-Qaeda, ta ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare a ƙasashen yammacin Afirka, har da wani mummunan hari da ta kai a filin jirgin saman jamhuriyar Nijar a watan da ya gabata, haɗe da kakaba takunkumi fetur a Mali.

Jaridar Washington Post ta ruwaito cewa Trump yana nazarin ko zai ɗauki wannan mataki ne a ƙasar Mali a daidai lokacin da ƙasar ke tsaka da gudanar da yaƙi da ƙasar Iran da ya shafe tsawon watanni.

Idan har aka amince, waɗannan hare-hare za su ƙara yawan ƙasashen da sojojin Amurka suka kai hari. A baya shugaban ya sa an kai hare-hare a ƙasashen Iraƙi, Nijeriya, Somaliya, Siriya, Venezuela, da Yemen.

Kara karanta wannan

Izala ta yi bayani kan karyar da aka yi wa Kabiru Gombe game da Tinubu

Shawarwarin jami’an gwamnati

Daga cikin jami'an gwamnatin da ke matsa lamba kan kai harin soji kan JNIM a Mali har da Sebastian Gorka, mataimakin mai taimaka wa shugaban ƙasa kuma babban daraktan yaƙi da ta'addanci a majalisar tsaron ƙasa.

Fadar White House ba ta tabbatar da cewa shugaban yana auna yuwuwar ɗaukar matakin sojin ba, sai dai wani jami'in gwamnati ya shaida wa kafafen yaɗa labarai cewa suna fatan ƙasashen kawancen Sahel za su yi nasara a kan ta'addanci.

Shugaban kasar Mali a Afrika
Shugaban Mali, Assimi Goïta na jawabi. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Trump ya kakaba wa Najeriya haraji

A wani labarin, mun rahoto cewa Amurka ta sanar da kakaba haraji kan kayayyakin da ake shigo da su daga ƙasashe 60, har da Najeriya, saboda gazawarsu wajen hana shigo da kayayyakin da aka samar ta hanyar tilasta wa mutane aiki.

Matakin wanda ofishin wakilin kasuwanci na Amurka (USTR) ya sanar a ranar Alhamis, ya ƙunshi ƙara harajin da kashi 10% ko kashi 12.5% ya danganta da manufofin kowace ƙasa a kan aikin tilas.

Najeriya tana cikin ƙasashen da za su fuskanci harajin kashi 12.5%, yayin da ƙasashen da ke da kyakkyawan tsarin hana aikin tilas za su fuskanci harajin kashi 10%.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng