Latest
INEC ta kayyade 19 ga Satumba 2026 domin gudanar da zaɓen ƙananan mazabu guda biyar a Gombe, Kano, Bauchi da Delta, ciki har da cike kujerar marigayi Yaya Tongo.
Ana kishin-kishin cewa Gwamnatin Nijeriya ta kulla yarjejeniyar tsagaita wuta da tsagerun Boko Haram karkashin jagorancin Bakura Doro domin dawo da zaman lafiya.
Kasar Iran ta ce ta kama jirgin ƙarƙashin ruwa mara matuƙi na Amurka a Mashigar Hormuz, yayin da Pentagon ta ce jirgin ya samu matsala tun da farko.
Shugaba Bola Tinubu ya yi jimamin rasuwar mataimakin darekta a Aso Rock, Peter Onwubuariri, wanda ya rasu yana dan shekara 48 bayan jinya, ya kuma yabi kokarinsa.
Gwamnatin Singapore ta sanar da ƙarin albashin ministoci da manyan jami’ai, inda Firaminista Lawrence Wong zai samu ƙarin albashi sama da kashi 60%.
Hakimin Dorayi a masarautar Kano, Alhaji Shehu Kabiru Bayero, ya yi bankwana da duniya a Masar, inda Masarautar Kano ta yi addu’ar Allah Ya ji kansa da rahama.
Gwamnatin Benue ta zargi Peter Obi da neman tayar da hankali bayan da aka toshe ayarin motocinsa yayin ziyararsa jihar ranar Talata 8 ga watan Satumbar 2026.
Yan adawar Isra’ila sun ce Benjamin Netanyahu bai cancanci ci gaba da zama firaminista ba bayan rahoton cewa UAE ta gargade shi kafin harin Hamas na 2023.
Jigon APC Hilliard Eta ya bukaci EFCC ta binciki Atiku Abubakar kan tsofaffin zarge-zargen laifukan kudi, yana mai cewa binciken ya kasance bisa hujjoji da doka.
Masu zafi
Samu kari