Sai Bango Ya Tsage: Yadda APC ke Ta Yi wa Kwankwaso Illa sakamakon Rikicin NDC a Kano

Sai Bango Ya Tsage: Yadda APC ke Ta Yi wa Kwankwaso Illa sakamakon Rikicin NDC a Kano

  • Shugaban APC na kasa ya dage sai ta raba Rufai Sani Hanga da Kabiru Ibrahim Gaya daga NDC
  • Jam’iyya mai mulki za ta iya yi wa Kwankwasiyya barna idan ta karbe tsofaffin sanatocin na Kano
  • Nentawe Yilwatda ya shiga ya fita domin ganin sun sauya-sheka duk da yana nuna ba haka abin yake

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda ya dage wajen karbe wasu daga cikin manyan ‘ya ‘yan jam’iyyar NDC.

APC mai mulkin Kano da Najeriya tana amfani da barakar da ke cikin NDC wajen ganin ta karya bayanta gabanin zaben 2027.

Kwankwaso
Sanata Rabiu Kwankwaso da wani da ya shigo NDC a gidansa a Kano Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

APC tana harin Rufai Hanga, Kabiru Gaya

Daily Trust ta yi bayanin yadda jam’iyyar APC ta shiga zarwarcin Sanata Rufa’i Sani Hanga da kuma Sanata Kabiru I. Gaya.

Farfesa Nentawe Yilwatda ya kai masu ziyara ne makonni bayan ya yi nasarar dawo da Sanata Ibrahim Shekarau cikin APC.

Kara karanta wannan

'Yan siyasan da suka ki barin jam'iyyar PDP har yau duk da rikicin cikin gida

Masu nazarin siyasa suna ganin wannan ziyara da ake yi da sunan hadin kan kasa ba komai ba ne illa jawo su jam’iyyar APC.

Nentawe Yilwatda ya zauna da Rufai Hanga sau biyu, a na karshen ya samu rakiyar abokin aikin sanatan, Barau Jibrin.

An yi wadannan zama ne lokacin da Sanata Hanga ya fito yana cewa da kamar wahala Peter Obi ya ci zaben Najeriya a NDC.

Kusancinsa da Rabiu Musa Kwankwaso bai sa ya samu tikitin Kano ta tsakiya ba, NDC ta tsaida Nasiru Yusuf Gawuna a 2027.

Kwankwaso ya maida wa Hanga martani

Rabiu Musa Kwankwaso ya tanka wa tsohon abokin tafiyarsa a siyasa a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin DITV.

‘Dan takarar mataimakin shugaban kasar ya fito yana cewa bai kamata mubaya’a ta rataya da abin da mutum zai samu ba.

Rabiu Musa Kwankwaso
Shugaban APC na kasa tare da Rufai Hanga da Kabir Gaya
Source: Facebook

Martanin Kwankwasiyya ga Sanata Hanga

Kakakin tafiyar Kwankwasiyya na kasa, Mansur Kurugu ya fada wa jaridar cewa wata tattaunawa a siyasa ba ta nufin sauya-sheka.

Kara karanta wannan

An ji labarin abin da aka tattauna da Peter Obi ya zauna da Jakadan kasar Switzerland

Malam Mansur Kurugu ya ce Kwankwasiyya jajirtacciyar tafiya ce wanda za ta iya tsaya wa da kafafunta ko da wani babba ya bar ta.

A nan ya bada misali da lokacin da suka rasa gwamnan jiha amma tafiyar ba ta jijjiga ba.

Wani jagora a APC ya yi magana yana cewa lokaci ya kure wa su Hanga da Gaya su iya samun takarar sanata a jam’iyyar APC.

Ko da sun sauya-sheka, APC ta gama tsaida ‘yan takarar sanata na jam’iyya. Amma hakan ba zai hana su yaki NDC a 2027 ba.

Ganduje ya yi kaca-kaca da Kwankwaso

An ji labari tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya soki shirin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso na tattaunawa da 'yan bindiga.

Ganduje ya bayyana cewa tattaunawa ko ba 'yan bindiga kudi zai kara karfafa musu gwiwa ne kawai wajen sayen makamai su yi ta ta'addanci.

Haka zalika ya yi hasashen cewa Kwankwaso da Peter Obi za su fadi zabe a 2027 saboda babu abin a zo a gani a tarihin mulkinsu na baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng