Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara bayan Kisan Manyan Yan Ta’adda 8 a Katsina

Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara bayan Kisan Manyan Yan Ta’adda 8 a Katsina

  • Rundunar sojojin Najeriya tare da sauran jami'an tsaro sun yi nasarar hallaka 'yan ta'adda takwas a jihar Katsina
  • Sojojin sun kai farmakin ne bayan samun sahihan bayanan sirri cewa mabiyan shugaban 'yan ta'adda Idi Abasu Aiki na shirin tare hanya domin kai hari
  • Rundunar soji ta tabbatar da ƙara sintiri da mamaye yankunan da abin ya shafa, tare da jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Dakarun rundunar sojin Najeriya tare da hadin gwiwar sauran jami'an tsaro sun kashe wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kashe yan ta'adda takwas a wani kwanton bauna da suka yi a ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina.

Sojoji sun kashe yan ta'adda a Katsina
Hafsan sojojin Najeriya, Laftanar Kanal Waidi Shaibu dadakarunsa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Nasarar da sojoji suka samu kan yan ta'adda

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Jiragen sojoji sun far wa taron 'yan bindiga 300 a jihar Zamfara

Bayan farmakin, rahoton Punch ya tabbatar da cewa sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu da babura biyar.

Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama'a na Rundunar Soji ta 17 Brigade, Kyaftin Abayomi Adisa ya ce an kai farmakin ne bayan samun bayanan sirri.

Adisa ya bayyana cewa bayanan sirrin sun nuna mabiyan fitaccen shugaban 'yan ta'adda Idi Abasu Aiki na shirin tare hanyar Kakumi zuwa Guga domin kai hare-hare kan matafiya marasa laifi.

Ya ce da isowar 'yan ta'addan, wadanda ke hawa babura biyar, sai aka yi musayar wuta mai tsanani tsakaninsu da dakarun soji.

Sojoji sun illata yan ta'adda a Katsina
Taswirar jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yawan yan ta'adda da sojoji suka kashe

A sakamakon wannan artabu, an kashe 'yan ta'adda takwas tare da kwato makamai da baburansu.

Adisa ya ce bayan kammala aikin, jami'an tsaro sun gudanar da bincike a yankin inda suka kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu da babura biyar.

Daga baya, an mika makaman da baburan da aka kwato ga rundunar 'yan sanda ta Bakori domin ci gaba da gudanar da bincike, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotu ta umarci a tsare malamin jami'ar ABU saboda kalaman da ya yi kan gwamnatin Katsina

Ya kuma bayyana cewa dakarun da ke sansanonin Ruwan Godiya da Mabai sun tsananta sintiri da mamaye wuraren da ake kyautata zaton 'yan ta'adda na amfani da su, domin dakile duk wani yunkurin kai hari.

Rundunar ta sake bai wa mazauna yankin tabbacin cewa tana ci gaba da sanya ido kan harkokin tsaro tare da daukar matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyi.

Ta ce dakarunta suna cikin shirin ko-ta-kwana domin dakile duk wata barazana da kuma ci gaba da fatattakar kungiyoyin 'yan ta'adda da ke aiki a Katsina.

Jami'an tsaro sun ragargaji yan bindiga

A wani labarin, an ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a wasu kauyukan karamar hukumar Charanchi da ke jihar Katsina.

Jami'an tsaro sun garzaya zuwa wurin da lamarin ya auku bayan samun labarin ta'asar da 'yan bindigan suka aikata a kauyukan guda biyu.

Saurin kai daukin da jami'an tsaron suka yi ya jawo sun samu nasarar dakile harin tare da kwsto dabbobi da dama da 'yan bindigan suka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.