Sojoji Sun Cafke 'Yar Kasar Waje Mai Safarar Kwayoyi ga 'Yan Ta'adda
- Dakarun Operation Hadin Kai sun kama wata 'yar kasar Chadi da ake zargi da safarar haramtattun kaya zuwa ga 'yan ta'adda
- Sojojin sun samu nasarar kwato hodar iblis, barasa da wasu kayayyakin da aka haramta da darajarsu ta kai miliyoyin naira
- Sojoji sun ce ana ci gaba da tsare wadda ake zargin kafin mika ta ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Dakarun rundunar Sector 3 na Joint Task Force North East, Operation HADIN KAI, sun kama wata mata 'yar kasar Chadi da ake zargi da safarar hodar iblis, barasa da wasu haramtattun kayayyaki zuwa ga 'yan ta'adda da ke boye a tsibiran Tafkin Chadi.
Dakarun sojoji sun kama wadda ake zargin ne a ranar Alhamis, 9 ga Yuli, 2026, yayin wani samame da dakaru suka gudanar a kan hanyar Maiduguri zuwa Monguno.

Kara karanta wannan
Nasara daga Allah: Jiragen sojoji sun far wa taron 'yan bindiga 300 a jihar Zamfara

Source: Twitter
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da mukaddashin jami'in yada labarai na hedikwatar Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a shafin X a ranar Juma'a, 10 ga watan Yulin 2026.
Kyaftin Mohammed Goni ya ce an cafke ta ne bayan tare wata mota mai tafiya zuwa Kwatan Doron Baga da ke karamar hukumar Kukawa a jihar Borno.
Sojoji sun bayyana wadda aka kama
Kyaftin Goni ya ce an gano wadda ake zargin da suna Rachael Samuel mai shekaru 48, 'yar Kelo da ke lardin Chari-Baguirmi a Jamhuriyar Chadi.
Ya bayyana cewa binciken farko ya nuna ana jigilar kayayyakin ne zuwa wasu wurare da ke cikin tsibiran Tafkin Chadi, yankin da aka san 'yan ta'adda na amfani da shi a matsayin maboyarsu.
Kayayyakin da aka kwato
Sanarwar ta ce kayayyakin da aka kwato sun hada da:
Kunshi bakwai na tabar wiwi da aka matse masu nauyin kusan kilo 30, gwangwani biyu na lita 10 dauke da sinadarin hydromercuric chloride da aka fi sani da "asha a mutu, kwalin giya daya dauke da kwalabe 48.
Sauran sun hada da kwalabe 61 na barasa, wayar hannu guda daya da kuma katin cirar kudi watau ATM guda biyu.

Source: Twitter
Wane mataki sojoji suka dauka?
Sojojin sun ce darajar kayayyakin da aka kwato ta kai miliyoyin Naira, inda suka kara da cewa ana ci gaba da bincike
A cewar sanarwar, wadda ake zargin tana hannun sojoji, yayin da aka adana dukkan kayayyakin da aka kwato kafin mika su ga hukumomin da abin ya shafa domin ci gaba da bincike da gurfanar da ita a gaban kotu bisa tanadin doka.
Rundunar ta kara da cewa wannan nasara ta nuna kudurin Operation Hadin Kai na dakile hanyoyin samar wa 'yan ta'adda kayan aiki da sauran kayayyakin da ke tallafa musu a yankin Arewa maso Gabas.
Cuta ta barke a sansanin 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa cutar amai da gudawa ta barke a wani sansanin 'yan ta'addan kungiyar ISWAP da ke yankin Timbuktu a Borno.
Barkewar cutar ta amai da gudawa ya yi sanadiyyar.kashe mayakan ISWAP guda tara bayan da aka kasa samar masu da magunguna.
Asali: Legit.ng
