Latest
Jam'iyyar ADC mai adawa ta ce Atiku Abubakar ba zai janye daga takarar 2027 ba, yayin da Chille Igbawua ya yi watsi da sukar shekarunsa da lafiyarsa.
Atiku Abubakar ya goyi bayan Dangote, yana mai cewa tallafin mai da ya gabatar zai rage kuɗin samar da mai a matatun cikin gida ba tare da jefa su cikin asara ba.
Isa Pantami ya koma PDP da goyon bayan Rainbow Coalition a Gombe, yayin da rahotanni ke nuna zai goyi bayan Tinubu amma ya kalubalanci APC a jihar.
Matatar Dangote ta ƙara farashin fetur daga N1,265 zuwa N1,350 kan lita yayin da farashin ɗanyen mai ke ci gaba da hauhawa a duniya saboda yakin Iran da Amurka.
Sanata Abdulaziz Yari zama lauyan shugaba Bola Tinubu, ya haska hikimar dokar haraji da cire tallafi. Darektan kamfen ya ce an kashe $7bn a sayen makamai.
Hukumar INEC ta bukaci kotu ta yi watsi da karar Atiku Abubakar kan takardun shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda rashin iko ko hakkin shigar da korafin.
Jigon jam'iyyar ADC, Chille Igbawua, ya yi wa Kwankwaso raddi cewa Atiku Abubakar ba zai janye daga takarar 2027 ba, yana mai kare shekarunsa da lafiyarsa.
Gwamna Inuwa Yahaya ya rantsar da manyan sakatarorin gwamnati 19 a Gombe, ya ce gwamnati za ta ɗauki sababbin ma’aikata tare da kammala biyan hakkokin ma'aikata.
Gwamna Soludo ya bayyana kyakkyawan fata cewa wa’adin mulki na biyu na Shugaba Bola Tinubu zai samar da “Najeriya mai ƙarfi da adalci”, duk da cewa Kwai wahalhalu.
Masu zafi
Samu kari