Ribadu Ya Bayyana Abin da ya Tattauna da Sabon Jami'in da Amurka Ta Aiko Najeriya
- Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya gana da sabon Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka mai kula da Afrika
- Frank Garcia, sabon jami'in da Amurka ta nada a Afrika ya zo kasar nan ne domin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu kan rashin tsaro
- Mashawarcin shugabanNuhu Ribadu ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da manyan jami'an manyan kasashen biyu suka tattauna
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya karɓi wata babbar tawaga daga Amurka.
Tawagar ta zo karsar nan a ƙarƙashin jagorancin sabon Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen ƙasar mai kula da nahiyar Afrika, Frank Garcia.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta kawo labarin cewa an gudanar da ganawar ne a Abuja a ranar Litinin 13 ga watan Yuli, 2026 domin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.
Jami'in Amurka ya zo Najeriya
Daily Post ta kawo labarin cewa Garcia ya isa Najeriya ne a karon farko tun bayan da aka rantsar da shi a ranar 1 ga Yunin 2026.
Ziyararsa na cikin rangadin da yake yi a yammacin Afrika daga ranar 11 zuwa 18 ga Yuli, 2026 inda zai kuma ziyarci Côte d’Ivoire da Mali.
Ya ce:
"A yayin da muke ƙarfafa haɗin gwiwarmu da Amurka, na karɓi wata babbar tawaga ƙarƙashin jagorancin sabon Mataimakin Sakataren Harkokin Afrika, Frank Garcia, a ziyararsa ta farko a hukumance zuwa Najeriya tun bayan da ya hau kan mukaminsa."
Amurka da Najeriya na karfafa dangantaka
Nuhu Ribadu ya kara da cewa an duba batutuwa da suka danganci inganta harkokin tsaro a sassan Najeriya da kuma hadin gwiwar tsaro.
Ribadu ya ƙara da cewa:
"Ganawar da muka yi ta ƙara ƙarfafa dangantaka mai ɗorewa tsakanin Najeriya da Amurka, tare da tantance ci gaban da aka samu ƙarƙashin Kwamitin Haɗin Gwiwa, sannan muka sake jaddada ƙudurimmu na zurfafa tattaunawa, haɗin kai da kuma fifita batutuwan tsaro da suka shafe mu gaba ɗaya."

Source: Getty Images
Ziyarar ta zo ne a lokacin da aka ake samun matsalolin tsaro musamman a Arewacin Najeriya inda yan ta'adda da yan bindiga ke kashe jama'a ba dare ba rana.
Trump ya tura Ribadu Amurka
A baya, mun wallafa cewa mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya tattauna batun yaki da ta'addanci da aka yi a Arewacin Najeriya tare da mataimakin shugaban Amurka.
Gwamnatocin Najeriya da Amurka sun ƙarfafa haɗin gwiwa wajen musayar bayanan sirri da kuma haɗin kan soja domin yaƙar Boko Haram yayin da Tinubu ya nuna godiya bisa ci gaba da tallafin horaswa da bayanan sirri.
A cewar sanarwar, tattaunawar ta sake tabbatar da haɗin kan da ke gudana tsakanin ƙasashen biyu wajen musayar bayanan sirri, horas da sojoji da gudanar da ayyukan yaƙi da ta’addanci.
Asali: Legit.ng