Duk da Adawarsu da Tinubu, An Yi Abin da sai da Atiku da Obi Suka Yaba Masa

Duk da Adawarsu da Tinubu, An Yi Abin da sai da Atiku da Obi Suka Yaba Masa

  • Alhaji Atiku Abubakar ya ce da aka fasa yin karin kudin jarrabawar SSCE, Gwamnatin tarayya ta yi abin yabo
  • ‘Dan takaran shugaban kasar ya ce tun farko babu dalilin da za a kawo wani kari da zai hana yara damar karatu
  • Shi ma Peter Obi yana da wannan ra’ayi, ya nemi gwamnati ta ba harkar ilmi muhimmanci a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya ji dadi da Gwamnatin tarayya ta fasa karin kudin jarrabawa.

A baya an ji labari cewa hukumomin WAEC da NECO za su yi karin kudin jarrabawar kammala sakandare ta SSCE a Najeriya.

Atiku, Obi da 'yan makaranta
Atiku Abubakar, Peter Obi da 'yan makaranta a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Atiku Abubakar ya yaba wa Gwamntin tarayya

Da jin labarin Gwamnatin tarayya ta bukaci a dakata da yin karin, Atiku Abubakar ya yi amfani da shafinsa na Facebook ya nuna farin cikinsa.

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan majalisar da ya yafe takara ya koma kasuwa ya dawo zai yaki Tinubu

Atiku Abubakar ya yi magana a ranar Litinin ya yabi wannan mataki bayan a baya ya fito ya soki yunkurin kara kudin NECO da WASSCE.

Phrank Shaibu ya fitar da jawabi a madadin ‘dan takarar shugaban kasar, ya ce bai kamata gwamnati ta zama mai gwajin manufofinta ba.

Atiku ya kira wannan mataki a matsayin nasara ga miliyoyin iyaye, dalibai, kungiyoyi masu zaman kansu da sauran ‘yan kasar Najeriya.

‘Dan takaran na NDC ya ce dakatar da karin ya wanke shi daga koken da ya yi a baya cewa hakan zai sa jarrabawar ta fi karfin talaka.

Bugu da kari, Atiku ya ce idan aka kara kudin jarrabawar, za a smu karin masu zaman banza kuma a hana yara zuwa manyan makarantu.

“Ana maraba da dakatarwar, sai dai ya jawo alamar tambaya; meyasa kullum sai gwamnatin nan ta ji mutane sun yi ca, kafin ta gyara manfofin da tun farko bai kamata a kawo su ba.
"Gwamnati ba dakin bincike ba ne na yin gwaje-gwaje na ganganci. Gwamnatin da ta san abin da ta ke yi, za ta tuntubi jama’a kafin ta yanke hukunci, ba sai bayan an jefa ‘yan Najeriya cikin dar-dar babu gaira babu dalili ba."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya shiga lamarin tsare El Rufai da barazanar kashe Peter Obi

- Atiku Abubakar

'Yan makaranta
Wasu 'yan makaranta suna karatu a Najeriya
Source: Getty Images

Peter Obi ya ji dadin fasa karin kudin SSCE

Jaridar Vanguard ta ce shi ma Peter Obi ya yi murna da jin wannan labari, ‘dan takaran na ADC ya kira lamarin da nasara ga miliyoyin ‘yan kasa.

Obi ya yi magana yana yaba wa gwamnati da ta saurari koken da al’umma suka yi kuma ya kawo shawara.

A shafinsa na X, ya ce kamata ya yi Gwamnatin Najeriya ta kara kudin da ta ke kashe wa a kan ilmi maimakon ta yi karin kudin jarrabawa.

“Na samu sa’ida da jin labarin dakatar da sabon karin kudin jarrabawa. Wannan nasara ce ga mutanen Najeriya.
"Duk da na yaba wa mahukunta da suka saurari koken jama’a wajen dakatar da tsarin, amma dole ne a fada cewa tun farko yin karin wani nauyi ne na babu gaira-babu dalili da bai kamata a kawo shi a lokacin da ake tsananin shan wahala ba"

Kara karanta wannan

Jirgin sama ɗauke da mataimakiyar shugaban ƙasa da wasu mutum 8 ya yi hatsari

- Peter Obi

Mista Obi ya yi kira ga gwamnati ta maida hankali wajen rage yaran da ba su zuwa makaranta, yana cewa ilmi hakkin duk ‘dan kasa ne.

Gwamnatin Sowore za ta maida ilmi kyauta

Labarin nan ya ce Omoyele Sowore ya gabatar da wata takardar manufofi mai ɗauke da matakai 20 da nufin sauya fasalin ilimi a Najeriya idan aka zabe shi.

Idan ya zama shugaban ƙasa, 'dan takaran ya ce wannan ba alkawarin siyasa ba ne kawai, aiki ne na gaske don ganin talauci bai hana yaro samun ilimi ba.

Ya ce ilimi zai kasance kyauta tun daga matakin firamare har zuwa jami'a. Haka kuma, gwamnati za ta ɗauki nauyin kuɗaɗen jarrabawar WAEC da NECO.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng