Akwai Matsala: Mataimakin Shugaban APC da Wasu Manyan Kusoshi Sun Fice daga Jam'iyyar

Akwai Matsala: Mataimakin Shugaban APC da Wasu Manyan Kusoshi Sun Fice daga Jam'iyyar

  • Mataimakin shugaban APC na Bauchi, Ibrahim Misau, tare da wasu shugabanni sun fice daga jam'iyyar zuwa PRP
  • Masu sauya shekar sun bayyana cikakken goyon goyon bayansu ga dan takarar PRPz Sanata Shehu Buba Umar a zaɓen gwamna na 2027
  • Sun zargi APC da kakaba 'yan takara da rashin bin tsarin dimokuraɗiyya yadda ya kamata a cikin jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Jam'iyyar APC reshen jihar Bauchi ta fuskanci babban koma baya bayan mataimakin shugabanta na jihar, Hon. Ibrahim Misau, ya sauya sheka zuwa PRP.

Ibrahim Misau ya koma PRP ne tare da wasu shugabannin APC na ƙaramar hukuma da na gundumomi a ƙaramar hukumar Misau gabanin zaɓen gwamnan jihar na 2027.

Jam'iyyar APC.
Tutar jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya Hoto: APC Nigeria
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito vewa Ibrahim Misau, tsohon ɗan Majalisar Wakilai na wa'adi biyu wanda ya wakilci mazaɓar Misau/Dambam, ya sanar da ficewarsa daga APC a hukumance.

Kara karanta wannan

"Tinubu zai sha kaye," An yi hasashen gwamnan da zai lashe zaben shugaban ƙasa a 2027

Dalilin da ya sa jiga-jigan suka bar APC

Masu sauya shekar sun ce sun bar APC ne saboda abin da suka kira ci gaba da kakaba 'yan takarar da ba su da farin jini da kuma rashin dimokuraɗiyya a cikin jam'iyyar.

Ƙaramar hukumar Misau ita ce mahaifar Ministan Lafiya da Walwalar Jama'a, Farfesa Muhammad Ali Pate.

Sun mara wa ɗan takarar PRP baya

Masu sauya shekar sun bayyana cikakken goyon bayansu ga ɗan takarar gwamna na PRP a zaɓen 2027, Sanata Shehu Buba Umar, suna mai cewa sun ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da adalci, gaskiya da shugabanci nagari.

A wani taro da Hon. Maiwada Bakoji Misau da Hon. Shehu Dubagari Misau suka shirya, masu sauya shekar sun bayyana matakin nasu a matsayin "farkawar siyasa" domin sake fasalin siyasar Bauchi.

Sun ce:

"Mun shiga PRP ne saboda siyasa ya kamata ta kasance don yi wa jama'a hidima, samar da damar ci gaba da kuma kawo ingantaccen ci gaba."

Kara karanta wannan

Soke zabubbukan ADC: Atiku ya aika sako ga magoya bayan jam'iyyar kan zaben 2027

Jawabin dan takarar gwamna na PRP

Yayin da yake tarbar sababbin mambobin, Sanata Shehu Buba Umar ya tabbatar musu da cewa za su samu dama iri ɗaya da sauran mambobin PRP.

Ya ce:

"PRP ta himmatu wajen tabbatar da adalci, haɗin kai, gaskiya da shugabanci mai fifita muradun jama'a. Mun shirya samar wa al'ummar Bauchi sahihin madadin shugabanci."

Ya kuma buƙaci magoya bayan jam'iyyar su ci gaba da haɗa kai da jajircewa yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ƙara ƙamari.

Jam'iyyar PRP.
Taron karbar tsohon mataimakin shugaban APC, Ibrahim Musau da wasu jiga-jigai a Bauchi Hoto: Mujaddadi TV
Source: Facebook

Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin wannan sauya shekar na iya ƙara ƙarfafa PRP aq jihar Bauchi tare da sauya yanayin siyasar jihar gabanin zaɓen gwamna na 2027.

Dalilin da ake ƙin Pantami da Shehu Buba

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya yabawa Ali Pantami da Sanata Shehu Buba da ke jihar Bauchi kan takarar da suke nema a zaben 2027.

Fitaccen malamin addinin musulunci ya ce abin takaici ne yadda ba a goyon bayan Pantami da Shehu Buba saboda kyawawan halayen da suke da shi.

Ya ce Pantami na fuskantar adawa da kiyayya saboda kawai shi malami yayin da ke ƙin Sanata Shehu Buba saboda yadda yke hada kan al'ummarsa ba tare da bambancin addini ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262