PFIPC: Kamfanin Amurka Ya Kawo Dauki ga Shugaban Hukumar Bogi da Ake Ta Surutu a Najeriya
- Kamfanin Von Batten-Montague-York ya bayyana cewa a shirye yake ya taimaka wa Adeniyi Adeyemi wajen neman mafaka a Amurka
- Ya ce an riga an sanar da wasu manyan jami'an gwamnatin Shugaba Donald Trump kan lamarin kafa hukumar bogi
- Kamfanin ya ce duk da babu wata doka da ta kafa PFIPC, amma yadda ta gudanar da ayyukanta ya nuna akwai alamar tambaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Kamfanin Von Batten-Montague-York, LC da ke Amurka ya tsoma baki kan badakar kafa hukumar Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC) ba tare da izinin gwamnatin Najeriya ba.
Kamfanin, wanda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya dauko haya, ya ce a shirye yake ya taimakawa Adeniyi Adeyemi wanda ake zargin ya jagoranci kafa hukumar bogi.

Source: Facebook
Wanda ya kafa kamfanin, Karl Von Batten, ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X yayin da yake martani kan rikicin da ya dabaibaye PFIPC.
Ya bayyana cewa a shirye yake ya taimaka wa Adeniyi Adeyemi, wanda ke fuskantar bincike daga hukumomin Najeriya, wajen neman mafakar siyasa da kariyar Amurka
Amurka za ta iya shiga lamarin PFIPC
Von Batten ya ce hukumomin Amurka za su iya shiga binciken lamarin saboda wani ɓangare na kasafin kuɗin Najeriya na samun tallafi daga rancen Bankin Duniya, wanda Amurka ita ce babbar mai ruwa da tsaki a cikinsa.
Ya ce duk da cewa PFIPC ba ta da wata doka da ta kafa ta ko kuma sanarwar shugaban ƙasa, ta gudanar da ayyukanta kamar hukumar gwamnati, inda aka ware mata kuɗi a kasafin 2026, ta samu ofis a sakatariyar tarayya tare da ɗaukar ma'aikata.
Kamfanin Amurka ya goyi bayan Adeyemi

Kara karanta wannan
PFIPC: Yadda 'yan sanda suka bankado ma'aikatar bogi a karkashin gwamnatin Tinubu
A wani saƙo da ya wallafa ranar Litinin, Von Batten ya ce ya tattauna da Adeyemi kuma ya gano cewa mutum ne mai gaskiya kuma abin yarda.
Ya ce zarge-zargen da Adeyemi ya yi sun isa su sa hukumomin Amurka su fara bincike kan wannana badaƙala.
Von Batten ya ce:
"Bayan tattaunawarmu, na yi imanin cewa zarge-zargen da ya gabatar sun cancanci Majalisar Dokokin Amurka, Ma'aikatar Harkokin Waje, Ma'aikatar Kuɗi da sauran hukumomin Amurka su bincika.
An gargadi gwamnatin Najeriya
Ya ƙara da cewa ya riga ya sanar da wasu manyan jami'an tawagar Shugaban Amurka Donald Trump game da lamarin, tare da bayyana cewa za su fara yi wa mambobin Majalisar Dokokin Amurka bayani a cikin wannan makon.
Kamfanin ya ce idan wani abu ya samu Adeyemi ko iyalansa yayin da yake shirin tattaunawa da hukumomin Amurka, za a ɗora alhakin hakan kan Shugaba Bola Tinubu kuma a nemi hukunta shi a Amurka.

Source: Twitter
Adeyemi ya aika sako ga Tinubu
An ji cewa shugaban hukumar bogi ta PFIPC, Adeniyi Adeyemi ya nuna rashin amincewa da bai wa hukumar ICPC umarnin bincikar badakalar ma'aikatarsa.

Kara karanta wannan
Adeyemi: Shugaban ma'aikatar bogi ya aika wasika ga Tinubu ana batun kai shi kotu
Ya bukaci a kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin gano gaskiya, yana zargin cewa gwamnatin tarayya ta riga ta wanke Femi Gbajabiamila.
A cewarsa, hanyar da ta fi dacewa wajen gano gaskiyar lamarin ita ce kafa kwamitin bincike mai zaman kansa, wanda ba shi da alaka da wata hukumar gwamnati.
Asali: Legit.ng
