'Buhari Ya Yi Mulki Irin Wanda Musulunci Ya Nemi a Yi': Alhassan Ado Doguwa

'Buhari Ya Yi Mulki Irin Wanda Musulunci Ya Nemi a Yi': Alhassan Ado Doguwa

  • Dan majalisar tarayya daga jihar Kano, Hon. Alhassan Ado Doguwa ya ce Najeriya ta yi babbar asara bayan rasuwar Muhammadu Buhari
  • Ya bayyana Buhari a matsayin shugaba mai gaskiya wanda bai tara wa kansa dukiya ba yayin da ya yi jagorancin kasar nan na tsawon shekaru takwas
  • Alhassan Ado Doguwa ya bayyana muhimmancin Buhari ga Najeriya da kuma irin asarar da kasa ta yi saboda rashin sa, musamman a halin da ake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Hon. Alhassan Ado Doguwa, ya ce rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta taba Najeriya.

Doguwa ya bayyana hakan ne yayin taron tunawa da cika shekara guda da rasuwar Buhari, wanda aka gudanar a Abuja a ranar Litinin 13 ga watan Yuli, 2026.

Kara karanta wannan

Yadda Kashim Shettima ya sharbi kuka a lokacin da Buhari zai rasu a asibiti

Alhassan Ado Doguwa ya fadi tuno ingancin Buhari
Marigayi Muhammadu Buharo, Hon Alhassan Ado Doguwa Hoto: Muhammadu Buhari/Alhassan Ado Doguwa
Source: Facebook

A wata hira da ya yi da BBC Hausa a gefen taron, Doguwa ya ce Buhari ya gudanar da mulkin Najeriya bisa koyarwar Musulunci da kuma adalci.

Buhari ya yi mulki da adalci - Doguwa

Da ya ke karin bayani a kan salon mulkin da Buhari ya yi Hon. Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar bai azurta kansa da dukiyar jama'a ba.

A kalamansa:

"Ya yi mulki irin wanda shari'ar Musulunci ta nemi shugabanni su yi, ba su so kansu ba, ba su tara wa kansu abin duniya ba."

Ya kuma ƙara da cewa:

"'Ya'yan da suka haifa tarbiyya suka ba su, suka bar sauran wa Allah SWT."

Doguwa: 'Najeriya ta yi rashin Buhari'

Hon Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa rasuwar Buhari ta zo ne a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙalubale masu yawa, inda ya ce ana bukatar irin shugabannin da za su ba da gudunmawar warware matsalolin ƙasa.

Kara karanta wannan

Taron tuna Buhari: Tinubu, Gowon, Shettima, Zulum da sauransu sun magantu

A cewarsa:

"Mai girma Muhammadu Buhari, a iya cewa an yi asararsa, Astagfirullah, a daidai wannan lokacin da ƙasar ta shiga irin yanayin da irinsu ake nema su bayar da gudunmawar da kila da an samu sauƙin abubuwan da ƙasar ke fuskanta."

A wajen taron, mahalarta sun yi jawabai kan rayuwar tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari, tare da tuna irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Najeriya tare da addu'ar Allah Ya kyauta makwancinsa.

Karibullah ya magantu kan Buhari

A baya, kun samu labarin cewa Sheikh Karibullah Nasiru Kabara ya bayyana irin dangantakar da ke tsakanin marigayi Muhammadu Buhari da malamai, musamman ta bangaren tunatar da shi nauyin da ke kansa.

Fitaccen malamin addinin Musulunci ya bayyana alakarsa da Buhari a ranar Litinin 13 ga watan Yuli, 2026 a taron tuna wa da tsohon shugaban kasar da ya shekara daya da komawa ga Allah SWT.

Sheikh Karibullah, wanda shi ne jagoran darikar Kadiriyya ya ce ya kan zauna daga shi sai Muhammadu Buhari sai Allah domin yi masa nasiha da tunatar da shi a kan hakkokin al'umma da ya lura da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng