Yadda Kashim Shettima Ya Sharbi Kuka a Lokacin da Buhari zai Rasu a Asibiti

Yadda Kashim Shettima Ya Sharbi Kuka a Lokacin da Buhari zai Rasu a Asibiti

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya tuna da lokacin da ya ziyarci tsohon shugaba Muhammadu Buhari a asibiti a London kafin rasuwarsa
  • Shettima ya ce ya fita daga dakin ICU yana kuka, ya kuma ce daukar gawar Buhari gida ya kasance daga cikin manyan abubuwa na rayuwarsa
  • YA fadi haka ne yayin da ake gudanar da bikin tunawa da marigayi Muhammadu Buhari a Abuja, inda manyan shugabanni Najeriya suka taru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya yi bayani mai ban mamaki a taron tunawa da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A bayani na musamman da ya yi, mataimakin shugaban kasar ya tuna da yadda ya kai ziyara a asibiti a birnin London kafin mutuwar Buhari.

Kara karanta wannan

'Buhari ya yi mulki irin wanda Musulunci ya nemi a yi': Alhassan Ado Doguwa

Kashim Shettima da Muhammadu Buhari
Kashim Shettima a hagu da Muhammadu Buhari a dama. Hoto: Bashir Ahmad|Kashim Shettima
Source: Facebook

The Nation ta wallafa cewa Shettima ya fadi haka ne a wajen taron tunawa da marigayi Buhari wanda aka yi a Abuja ranar Talata, 14 ga Yuli 2026.

Kashim Shettima ya yi kuka

Yayin da ya ke tuna kwanakin ƙarshe na tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a wani asibiti da ke Landan a bara, Kashim Shettima, ya ce ya fashe da kuka lokacin da ya ga rayuwar marigayin na gab da ƙarewa.

Da yake jawabi a wajen taron cika shekara guda da rasuwar Buhari a jiya, Shettima ya ce:

“Shugaban Ƙasa (Bola Ahmed Tinubu) ya kira ni ya ce, ‘Kashim, yanzu na samu labarin cewa shugaba Muhammadu Buhari ba shi da lafiya a London. Don Allah ka tafi London ka gano halin da yake ciki, kuma ka tabbatar bai rasa komai ba.’”

Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana irin yanayin da ya gani a asibitin da ke London, wanda ya ce ya sanya shi zubar da hawaye.

Kara karanta wannan

Taron tuna Buhari: Tinubu, Gowon, Shettima, Zulum da sauransu sun magantu

“Na fito daga ɗakin, hawaye cike da idanuna, sannan na tarar da Zara da Yusuf ('ya'yan Buhari) a ƙofar ICU. Abu ne mai matuƙar taɓa zuciya. Lokaci ne mai cike da tausayi,”

In ji Shettima.

Shettim da Aisha Buhari a Abuja
Kashim Shettima a wajen tunawa da Muhammadu Buhari. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Shettima ya dawo da Buhari

Shettima ya ƙara da cewa raka gawar marigayi Shugaba Buhari zuwa gida domin birne ta na daga cikin manyan karramawar da ya taɓa samu a rayuwarsa.

Marigayi tsohon shugaban ƙasar ya rasu a Landan a ranar 13 Yulin 2025 a London, daga bisani aka dawo da gawarsa Najeriya, inda aka birne shi a gidansa da ke Daura, jihar Katsina.

'Yan uwa da iyalan marigayin, abokan siyasarsa ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, abokan aikinsa na soja da waɗanda ya taɓa jagoranta sun halarci taron tunawa da shi.

Punch ta wallafa cewa taron ya samu halartar manyan baƙi, ciki har da tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon, shugabannin majalisar dokoki, gwamnoni, sarakunan gargajiya da sauransu.

Bayanin Bola Tinubu

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaba Tinubu, wanda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya wakilta, shi ne ya fara gabatar da bayani a taron tuna Buhari.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya nema a wurin Sheikh Karibullah a lokacin yana shugaban kasa

Yayin da yake gabatar da jawabin shugaba Tinubu, Shettima ya tabbatar wa iyalan marigayin cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da kasancewa tare da su a kowane lokaci.

Da yake magana kai tsaye ga uwargidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari, da 'ya'yanta, shugaban kasar ya ce ba za a manta da su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng