'Ko Gida Ban Mallaka ba a Shekaru 8': Tsohon Gwamna Ya Bugi Kirji

'Ko Gida Ban Mallaka ba a Shekaru 8': Tsohon Gwamna Ya Bugi Kirji

  • Sakataren jam'iyyar ADC na ƙasa, Rauf Aregbesola, ya tuna yadda ya mulki jihar Osun tsawon shekaru takwas
  • Aregbesola ce ya shafe shekaru takwas yana mulkin Osun ba tare da mallakar gida nasa ba, yana zaune a gidan abokinsa
  • Gwamnan ya ƙalubalanci duk mai musanta ikirarinsa da ya fito ya nuna gidan da ya mallaka lokacin yana gwamna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola ya ce tsohuwar gwamnatinsa ta mayar da hankali kan rage talauci, yunwa, rashin aikin yi.

Aregbesola ya bayyana cewa ya shafe dukkan shekaru takwas yana gwamnan Osun yana zaune a gidan wani abokinsa.

Aregbesola ya kafa tarihi lokacin da ya ke gwamna
Tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola da ya koma ADC, Rauf Aregbesola.
Source: Twitter

Ɓangaren da Aregbesola ya ba fifiko lokacin mulkinsa

A cikin wani bidiyo da Punch ta bibiya, Aregbesola ya waiwayi shekarunsa na mulki tare da bayyana abubuwan da gwamnatinsa ta ba fifiko wajen gudanar da ayyuka.

Kara karanta wannan

'Yabon Trump ya nuna aikinmu ya na kyau': Fadar shugaban kasa

Sakataren ƙasa na jam'iyyar ADC, Aregbesola ya ce cewa bai mallaki gidan kansa ba a lokacin mulkinsa.

A cewarsa, shi ne gwamna na farko a Najeriya da ya yi mulkin jiha na tsawon shekaru takwas ba tare da mallakar gida nasa ba.

Ya ce ya zauna a gidan wani abokinsa tsawon shekaru takwas yana gwamna a ƙasar mahaifinsa, yana mai ƙalubalantar duk wanda ya ce ba gaskiya yake faɗa ba.

Ya bayyana cewa:

“Ni ne gwamna na farko a Najeriya da ya yi mulkin jiha na tsawon shekara takwas ba tare da mallakar gida na kaina ba.
“Na zauna a gidan abokina na tsawon shekara takwas ina gwamna a garin mahaifina, duk wanda ya ce abin da nake faɗa ba gaskiya ba ne, ya fito ya nuna min gidan da na mallaka.”
Tsohon gwamna ya bayyana tarihin da ya kafa a mulkinsa
Sakataren jam'iyyar ADC na kasa, Rauf Aregbesola ya halarci taro a Lagos. Hoto: Rauf Aregbesola.
Source: Facebook

Aregbesola ya kalubalanci jama'a kan kalamansa

Aregbesola ya ce duk wanda ke musanta ikirarinsa ya fito fili ya nuna gidan da ya mallaka a lokacin da yake riƙe da muƙamin gwamnan Osun, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya bayyana matsayar Kano kan kafa 'yan sandan jiha

Tsohon ministan harkokin cikin gida a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jagoranci Osun daga shekarar 2010 zuwa 2018.

Yayin da yake waiwayen mulkinsa, Aregbesola ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen inganta rayuwar al'umma ta hanyar aiwatar da manufofin rage talauci, yunwa da rashin aikin yi.

Aregbesola ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta kuma ba fifiko ga inganta kiwon lafiya, samar da ingantaccen ilimi, tabbatar da zaman lafiya tsakanin al'umma da kuma bunƙasa ci gaban Osun.

Aregbesola ya shirya kifar da Tinubu

Mun ba ku labarin cewa sakataren jam’iyyar ADC, Rauf Aregbesola, ya yi ikirarin cewa jam’iyyarsu za ta hambarar da Shugaba Bola Tinubu a 2027 da ake tunkara a Najeriya.

Aregbesola ya bayyana cewa ADC za ta kwace Lagos da fadar gwamnati ta Abuja a babban zaɓen 2027 da ke tunkarar kasar wanda ake hasashen zai yi zafi sosai.

An kuma samu wata ƙungiya mai suna Conscience Forum daga LP ta koma ADC a lokacin da ta cika shekaru 25 da kafuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.