Trump Ya Gindaya Sharuda ga Saudiyya game da Isra'ila bayan Ƙulla Yarjejeniya

Trump Ya Gindaya Sharuda ga Saudiyya game da Isra'ila bayan Ƙulla Yarjejeniya

  • Shugaba Donald Trump ya ce yarjejeniyar makamashin nukiliyar Amurka da Saudiyya za ta tabbata ne idan Riyadh ta amince da Isra'ila
  • Trump ya jaddada cewa Saudiyya ba za ta riƙa tace sinadarin uranium ba, yana mai cewa shirin ya shafi amfani da makamashin nukiliya cikin lumana kawai
  • Saudiyya ta sha bayyana cewa ba za ta amince da Isra'ila ba sai an kafa ƙasar Falasdinu, yayin da Isra'ila ta yaba da sabon sharadin Trump

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka Donald Trump ya yi magana game da yarjejeniyar da suka kulla da kasar Saudiyya.

Trump ya bayyana cewa yarjejeniyar haɗin gwiwar makamashin nukiliya tsakaninsa da Saudiyya za ta samu amincewa ne kawai idan Riyadh ta shiga Yarjejeniyar Abraham tare da amincewa da ƙasar Isra'ila.

Kara karanta wannan

Shirin Amurka na samar wa Saudi nukiliya ya firgita 'yan Isra'ila

Trump ya gindaya sharadi ga Saudiyya
Shugaban Amurka Donald Trump tare da Mohammed Bin Salman Hoto: Chip Somodevilla.
Source: Getty Images

Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social bayan kulla yarjejeniya da Saudiyya.

Ya ce yarjejeniyar ta shafi amfani da makamashin nukiliya cikin lumana kawai, kuma ba za a ba Saudiyya damar tace sinadarin uranium ba.

Kalaman Trump sun zo ne bayan wasu masana sun nuna damuwa cewa irin wannan yarjejeniya na iya ƙara haɗarin yaɗuwar makaman nukiliya a yankin Gabas ta Tsakiya.

A baya Saudiyya ta bayyana cewa ba za ta amince da Isra'ila ba sai an fara kafa ƙasar Falasdinu mai cin gashin kanta.

Wannan matsaya ta kasance ba ta sauya ba har zuwa yanzu.

A shekarar 2020, Trump ya jagoranci cimma Yarjejeniyar Abraham wadda ta sa Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain suka daidaita hulɗa da Isra'ila.

Daga baya Sudan da Morocco da Kazakhstan su ma suka rattaba hannu, sai dai har yanzu Saudiyya ba ta mayar da martani kan kalaman Trump ba.

Kara karanta wannan

'Mun rike wuta': Ministan Amurka ya yi Ikirarin Iran na rokon a yi sulhu

Haka kuma ba a bayyana cikakken rubutun yarjejeniyar ba domin a tabbatar ko wannan sharadi yana cikin takardarta.

A gefe guda, ofishin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yaba da furucin Trump.

Ya ce idan Saudiyya ta shiga Yarjejeniyar Abraham, hakan zai zama babban ci gaba wajen samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Ma'aikatar Makamashi ta Amurka ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta ba kamfanonin Amurka damar shiga shirye-shiryen makamashin nukiliya na Saudiyya domin amfani da makamashi cikin lumana.

Tun a shekarar 2018, Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya ce Saudiyya ba ta da shirin mallakar makamin nukiliya.

Sai dai ya ce idan Iran ta mallaki irin wannan makami, Saudiyya ma za ta bi sahu cikin gaggawa.

Trump ya kuma bayyana cewa yarjejeniyar za a aika ta zuwa Majalisar Dokokin Amurka domin tantancewa. Duk da ana sa ran wasu 'yan majalisa za su yi adawa, jam'iyyar Republican na da rinjaye a majalisun biyu.

Trump ya yi barazana ga Iran

Mun ba kula labarin cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba mallakar makamin nukiliya ba.

Kara karanta wannan

'Yabon Trump ya nuna aikinmu ya na kyau': Fadar shugaban kasa

Donald Trump ya yi barazanar lalata gada ko tashar samar da wutar lantarki a duk lokacin da Iran ta kai hari kan jirgi a mashigar Hormuz.

Shugaba Trump ya kuma bayyana cewa Amurkawa ba sa adawa da yakin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.