Sojoji Sun Yi Babban Kamu a Borno, Sun Cafke Ɗan Ƙasar Waje dake Tallafawa ISWAP

Sojoji Sun Yi Babban Kamu a Borno, Sun Cafke Ɗan Ƙasar Waje dake Tallafawa ISWAP

  • Dakarun Operation HADIN KAI sun kama wani ɗan Sudan da wasu mutum uku da ake zargi da taimaka wa ƙungiyar ISWAP a Borno da Yobe
  • Sojoji sun ce bayanan sirri ne suka taimaka wajen cafke waɗanda ake zargi, tare da ƙwato kayayyakin da ake zargin na tallafa wa ayyukan ta'addanci
  • Dakarun sun ce nasarar ta nuna ci gaban da ake samu wajen dakile shigowar mayaƙan ƙasashen waje da karya hanyoyin tallafa wa ISWAP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Borno - Dakarun Operation HADIN KAI sun yi nasarar cafke wani dan kasar Sudan da ake zargi da alaƙa da ƙungiyoyin ta'addanci.

Hakazalika, bayanai sun nuna cewa sojoji sun kuma kama wasu mutum uku da ake zargi masu haɗa kai da ƙungiyar ISWAP a jihohin Borno da Yobe.

Sojoji sun cafke dan kasar Sudan da ke tallafawa 'yan ta'adda a Borno.
Sojoji sun tasa keyar dan kasar Sudan da suka kama bisa zargin tallafawa 'yan ta'adda. Hoto: @BeautifulNGA (X)
Source: Twitter

Yadda sojoji suka kama dan kasar Sudan

Kara karanta wannan

An gwabza kazamin fada da 'yan ta'addan ISWAP suka farmaki sansanin sojoji a Borno

Rahotannin da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya samu a ranar Litinin sun bayyana cewa, kamen ya biyo bayan bayanan sirri da dakarun suka samu, wanda ya kai ga gudanar da farmaki a wurare daban-daban na yankin Arewa maso Gabas

Rahoton ya ce dakarun Bataliya ta 115 sun kama wani dan Sudan mai suna Musa Fashir, mai shekara 32, a yankin Lassa-Dille da ke ƙaramar hukumar Askira/Uba ta jihar Borno

Binciken farko ya nuna cewa ana zargin Fashir na da alaƙa da wasu 'yan ta'adda, lamarin da ya ƙara nuna yiwuwar shigowar mayaƙan ƙasashen waje domin taimaka wa ayyukan ta'addanci a yankin

Cafke masu tallafa wa ISWAP

Haka kuma, dakarun sun kama wata mata mai suna Mary Florence, mai shekara 36, wadda ta ce ita baƙuwa ce daga ƙasar Ghana ba tare da takardun izini ba.

Jami'an tsaro na ci gaba da bincike domin tabbatar da asalinta da kuma ko tana da wata alaƙa da ayyukan ta'addanci ko wasu laifuka

A wani samame daban, dakarun Brigade ta 27 tare da haɗin gwiwar Civilian Joint Task Force (CJTF) sun kama wani da ake zargin mai haɗa kai ne da ISWAP a yankin Shishiwaji da ke ƙaramar hukumar Gulani ta jihar Yobe

Kara karanta wannan

Tarihin yadda aka assasa rundunar sojin Najeriya da Hausawa 18 a Legas

Rahoton Punch ya nuna cewa ana zargin mutumin mai haƙar ma'adinai ne ba bisa ƙa'ida ba, kuma yana da alaƙa da ISWAP. An kama shi da wayoyin hannu guda uku

Har ila yau, yayin sintirin kare manoma a yankin Kasabalari da ke ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno, dakaru sun kama wasu mutum biyu da ake zargin suna samar wa ISWAP kayan aiki.

Sojoji sun kama wasu da ake zargin suna tallafawa 'yan ta'adda a Borno da Zamfara
Dakarun sojojin Najeriya a kan tankar yaki suna aikin kakkabe 'yan ta'adda a daji. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojoji sun dage wajen yaki da ta'addanci

Kayan da aka kwato daga hannunsu sun haɗa da kekuna biyu, wayar hannu guda ɗaya, katin shaida, magungunan kashe kwari, magunguna, kayan gyaran keke, na'urar hasken rana, fitilar hannu da kuma wuƙaƙe

Jami'an sojin sun bayyana cewa waɗannan nasarori sun nuna yadda amfani da bayanan sirri ke taimakawa wajen dakile shigowar mayaƙan ƙasashen waje, rushe hanyoyin samar da kayan aiki ga 'yan ta'adda da kuma karya cibiyoyin masu mara musu baya a yankin Arewa maso Gabas

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com